Kocin kungiyar kwallon kafa ta Akwa United da ke Akwa Ibom, Zakary Baraje ya ce zai daina horar da kungiyar muddin ba ta sayo sababbin ’yan kwallo kafin a fara gasar rukuni-rukuni ta Najeriya ba.
Kocin ya bayyana haka ne ga menama labarai jim kaan bayan kulob in ya samu nasarar lashe kofin kalubale na kasa (Federation Cup) bayan ya lallasa kulob in Lobi Stars da ci 2-1 a wasan karshe da ya gudana a filin wasa na Teslim Balogun dake Lagos a ranar Lahadin da ta wuce.
Kocin ya bayar da shawarar a cigaba da rike ’yan kwallon da suka samu nasarar lashe wannan kofi inda ya bukaci a haa su da sababbin da za a sayo nan gaba don karfafa musu gwiwa.
Baraje ya ce “kimanin shekara 56 kenan da wani kulob da ya fito daga Jihar Kuros Riba ko Akwa Ibom ya samu nasarar lashe wannan kofi, sai a wannan karo da na jagoranci kulob in kuma Allah Ya ba ni nasara”.
Yanzu kulob in Akwa United zai fafata a gasar cin kofin kalubale na Afirka da Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) take shiryawa.
Zan daina horar da Akwa United muddin ba ta sayi sababbin ’yan kwallo ba – Zakary Baraje
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Akwa United da ke Akwa Ibom, Zakary Baraje ya ce zai daina horar da kungiyar muddin ba ta sayo sababbin…