Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce yana da yakinin zai bar kasar a karshen wa’adinsa a 2023 fiye da yadda ya karbe ta a 2015.
Ya ce ya zuwa yanzu, an kassara matsalar rashawa ta yadda ’yan Najeriya na kwarmata batutuwan rashawa ba tare da wani tsoro ba, sannan an yi nasarar kwato makudan kudaden gwamnati da aka wawushe.
- Za a ragargaje babura 250 da aka kwace a Legas
- DAGA LARABA: Halin da karatun Boko ke ciki a Jihar Bauchi
Haka nan, Buhari ya ce an karya lagon ’yan ta’adda ta yadda a yanzu babu kowane bangare na kasa da ke hannunsu, an kuma karkashe shugabanninsu, kana ayyukan gina kasa na gudana don ci gaba da bunkasa Najeriya.
Shugaba Buhari ya yi wadannan bayanan ne a matsayin martani ga tambayar da jaridar Bloomberg ta yi masa kan ko yaya zai bayyana kokarinsa wajen cika alkawuran da ya yi wa talakawansa?
Yaki da cin-hanci da rashawa, tada komadar tattalin arziki da inganta fannin tsaron kasa na daga cikin alkawuran da Buharin ya yi wa ’yan Najeriya a lokacin da yake yakin neman kuri’unsu.
Ya ce a 2015, Boko Haram na rike da wurare da daman gaske a garuruwan da ke kan iyakokin kasa, amma daga bisani an kwato duka yankunan da lamarin ya shafa.
Ya kara da cewa, irin kayan aikin da gwamnatinsa ta mallaka da kuma kokarin da gwamnatin tasa ke yi a fagen yaki da ta’addancin, ba a ga irin haka ba a gwamnatin da ya gada.
Kazalika, bayanan Buhari sun tabo irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a sauran fannoni da suka hada da fannin noma da kiwo da lantarki, tattalin arzikin kasa, ayyukan gina kasa, kiwon lafiya, kyautata mu’amala tsakanin Najeriya da kasashen duniya, da sauransu.