Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce zai tabbatar da cewa ya bar Najeriya cikin yanayi mai kyau fiye da yadda ya karbe ta, sannan ya roki ’yan Najeriya su yi adalci wajen bayyana nasarorin gwamnatinsa.
Buhari ya bayyana cewa ya ce yana da kyau a yi masa adalci kan alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe a shekarar 2015.
- Najeriya A Yau: Yadda Tsaro Da Tattalin Arziki Za Su Shafi Zaben 2023
- ’Yan bindiga sun kai hari a sansanin soji a Katsina
A ranar Alhamis ne ya yi kiran a yayin da yake ziyarar kwana biyu domin kaddamar da wasu ayyuka da Gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai ta yi a Jihar Kaduna.
Da ya ke jawabi a fadar sarkin Jema’a, Alhaji Muhammadu Isa II a Kafanchan, Shugaba Buhari ya ce, zai tabbatar gwamnatinsa ta inganta harkar siyasa da rayuwar al’umma.
Sannan ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da ’yan sanda da sojoji wajen kawo karshen matsalar tsaro, don sake sanya karsashi a zukatan ’yan Najeriya.
“Babu wanda za a bari ya dauki makami ya kai wa mutane farmaki, ba su ji ba, ba su gani ba,” a cewar Buhari.
Tun da farko Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya jinjina wa Buhari kan kokarin da yake yi na ganin an kawo karshen ayyukan ’yan bindiga musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda ya ce yankin Kafanchan ya samu zaman lafiya fiye da yadda yake a baya.
Shi ma da ya ke nasa jawabin, Sarkin Jama’a ya bukaci a girke dakarun sojin da za su rika yin sintiri da kuma jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma domin tabbatar da zaman lafiya a yankin na Kafanchan.