✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kori duk ma’aikacin da ya fitar da bayanai ba bisa ka’ida ba — Gwamnati

Shugabar Ma’aikata na Gwamnati ta Najeriya, Folasade Yemi-Esan ta bayyana takaici game da yawan fitar da bayanan gwamnati na sirri ba bisa ka’ida a kafafen…

Shugabar Ma’aikata na Gwamnati ta Najeriya, Folasade Yemi-Esan ta bayyana takaici game da yawan fitar da bayanan gwamnati na sirri ba bisa ka’ida a kafafen sada zumunta.

Folasade ce abin kunya ne yadda ake fitar da wadansu bayanan da dauke da sa hannun manyan jami’an gwamanti.

Da take cewa gwamnati ba za ta lamunci hakan ba, Folasade ta yi barazanar sallamar duk ma’aikacin da aka kama da aikata laifin.

A wani sakon da Darakta Mai Kula Yada Bayanai, Mrs Olawunmi Ogunmosunle ta ce koken na Shugabar Ma’aikatan na dauke ne cikin wani bayani da ta fitar a ranar 22 ga watan Mayu.

Ta ce “Abun takaici ne kuma ya saba ka’idar aiki wanda za a iya korar ma’aikaci a dalilinsa a karkashin Dokar Aikin Gwamnati Lamba ta 030401 da 030402”

Ta yi barazar cewa, nan gaba duk ma’aikacin gwamnati da aka kama da aikata irin wannan laifin zai fuskanci hukunci daidai da tanadin doka.

Dokta Yemi-Esan ta kuma bukaci manyan sakatarorin ma’aikatu da su ja kunnen ma’aikatansu a kan bayanin da ke sulalewa da kuma hukuncin da gwamnati ka iya dauka a kan duk wanda ya yi wa dokar karan tsaye.

A kwanakin da suka gabata ne kwafin jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar a kan annobar coronavirus ta fita kuma ta yadu a kafafen sada zumunta tun kamin gabatar da shi.

Daga baya Mai Taimaka wa Shugaban a kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya bayyana cewa an gano wanda ya aikata hakan.