Daruruwan al’ummar Zamfarawa sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Sakkwato saboda sake karuwar hare-haren ’yan bindiga a Jihar Zamfara.
Fusatattun magidanta da mata da kananan yara daga kauyen Bingi da kewaye a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, dauke da ganye sun hana zirga-zirgar ababen hawa, tare da neman a tura jami’an tsaro a yankunan nasu da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.
- An kama magidanci ya je kwartanci wurin matar amininsa
- Ana dab da fara cinikin filin jirgin saman Abuja, Kano da wasu guda 2
Wasu daga cikinsu sun shaida mana cewa sun kwaso kayansu da ’ya’yansu da matansu sun baro kauyukansu ne saboda janye jami’an tsaron da gwamnati ta yi.
“Kwanan nan hare-haren ’yan bindiga sun karu a kauyukanmu, tun da ’yan bindiga suka lura an janye sansanonin jami’an. Yanzu haka kauyuka sama da 10 ne suka tsere saboda farmakin ’yan bindiga.
“Ba za mu koma ba sai an dawo mana da jami’an tsaron. Ko sun manta cewa yankunanmu ne ke cikin babbar matsala? Sai sacewa da kashe mana mutane ake yi kusan kullum.
“Ba tura jami’an tsaron kawai ba, gwamnati ta kara yawansu, saboda maharan da ke mamaye kauyukan namu da yawan gaske suke zuwa, saboda haka akwai bukatar wadatattun jami’an tsaron da za su tunkare su,” inji wani mazaunin yankin.
Wakilinmu ya yi ta kokari, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ya kasa samun kakakin ’yan sanda a Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, domin jin ta bakinsa.