Ya ku ’yan uwana al’ummar Jihar Zamfara, wannan wani muhimmin sako ne nake son isarwa zuwa gare ku baki daya tsakanina da Allah, da kuma irin yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fahimtar da ni gwargwado, game da abin da yake gudana na siyasar jiharmu mai albarka. Ya ku ’yan uwana! Zan ba ku wannan shawara ne, ba don siyasa ba, ba don wani abin duniya ba. A’a, sai dai domin kishina ga jihata, tare da bakin cikina kan matsalar tsaro da muke fama da shi. Kuma alhamdulillahi, ko hasidin iza hasada ya san cewa, yanzu Gwamna Matawalle yana kokari matuka a kai. Muna rokon Allah Ya ci gaba da agaza masa, Ya ci gaba da taimakonsa a kan wannan kokari da yake yi, amin.
Ya ku Zamfarawa! Ku ji tsoron Allah, ku sani, ya zama dole ku bayar da duk goyon bayanku ga Gwamna Matawalle. Ina tabbatar muku cewa ban san Gwamna ba kuma bai san ni ba, ban taba ganinsa ba, ban taba yin wata hulda da shi ba, amma ina tabbatar muku Gwamna Matawalle mai kishinku ne, mai tausayinku ne, mai son ci gaban Jihar Zamfara ne.
Don haka ya zama dole ku taimaka masa, ku ba shi duk irin goyon baya da hadin kai da yake nema daga wurinku. Sannan ina jan kunnenku, da kada ku yarda da duk masu yi wa Gwamnan zagon kasa da sunan siyasa ko adawa.
Dukkanku kuna sane da halin da jiharmu take ciki na kalubalen tsaro da talauci da rashin ingantaccen ilimi da rashin abubuwan more rayuwa. Dukkanku kuna sane da halin kaka-ni-ka-yi da jiharmu ta shiga, sanadiyyar halin ko in kula da zalunci, da gwamnatin da ta shude ta jefa jihar a ciki.
Mun yi addu’o’i, mun yi ta azumi da alkunuti, domin Allah Ya dube mu da idon rahama, Ya kawo mana canji na alheri, Ya kawo mana shugaban da muke so, yake sonmu irin shugaban da Manzon Allah (SAW) ya siffanta a cikin Hadisin Ka’ab dan Malik da ke cikin Sahih Muslim.
Daga zuwan wannan bawan Allah, mun ga canji, aiki ba kama hannun yaro, biyan albashi ba wasa, ya mayar da hankali sosai wurin ganin jiharmu ta samu cikakken tsaro mai dorewa.
Sai ga shi an samu wadansu miyagun ’yan siyasa, wadanda su ne suka jefa jihar cikin mummunan hali a can baya, saboda salon mulkinsu irin na fir’aunanci, suna sukar kokarin da wannan bawan Allah yake yi. Har na samu labari daga majiya kwakkwara, wadannan miyagun ’yan siyasa, za su yi duk mai yiwuwa su ga cewa wai sun kawo cikas ga duk kokarin da Gwamna Bello Matawalle yake yi a jihar.
Don haka, muna isar da sako zuwa ga wadannan miyagun ’yan siyasa su sani cewa, ta Allah ba ta su ba. Kuma Zamfarawa ba wawayen mutane ba ne, za su yi iya kokarinsu domin ganin sun bai wa wannan bawan Allah goyon baya, don ciyar da jiharmu mai albarka gaba. Duk wani yunkuri nasu na sharri da duk wani makirci, da yardar Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) ba za su taba cin nasara ba. Allah zai taimaki Gwamna Matawalle da Zamfarawa da Jihar Zamfara a kansu. Domin yanzu kifi yana ganinka mai jar koma.
Al’ummar Jihar Zamfara, ku sani, Gwamna Matawalle na bukatar goyon bayanku da gudunmawarku, da hadin kanku, domin ya kawo ci gaba mai dorewa a wannan jiha tamu mai albarka. Kada ku yarda da ’yan damfara da sunan adawar siyasa, kada ku yarda da duk wani da zai mayar muku da hannun agogo baya. A tarihin Jihar Zamfara, Gwamnan Mulkin Soja, Kanar Jibril Bala Yakubu ya yi kokari matuka, a lokacin da yake Gwamna. Haka, bayan shigowar siyasa, Gwamna Ahmad Sani Yariman Bakura shi ma ya yi iya nasa. Haka Gwamna Mamuda Aliyu Shinkafi ma ya yi kokari matuka. Amma wallahi, Gwamna Abdul’azizi Yari, babu abin da ya yi in ba ruguza Jihar Zamfara ba.
Mu ba ruwanmu, duk mutumin kirki za mu bayyana shi domin mutane su san shi kuma su so shi, su yi masa addu’a da fatan alheri. Haka mutumin banza za mu bayyana shi domin mutane su guje shi, kuma su yi Allah wadai da mugun halinsa.
Zamfarawa ku yi hattara, Gwamna Matawalle lallai ya nuna muku halacci, saboda haka ya zama dole ku nuna masa halacci. Kada ku yarda da duk wani mai soki-burutsu, mayaudari wanda zai nuna muku cewa Gwamna Matawalle mutumin banza ne. Duk wanda ya gaya maku haka ku ce karya yake yi, ko shi wane ne domin kun gani a kasa.
Allah Ya taimake mu, Ya zaunar da yankinmu na Arewa lafiya, Ya zaunar da jiharmu ta Zamfara lafiya, da dukkan sauran jihohi da Najeriya baki daya, amin.
Dan uwanku Imam Murtada Muhammad Gusau, Okene, Jihar Kogi
08038289761, imel: [email protected]