✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buni ya gabatar da N320bn kasafin Yobe na baɗi

Kasafin kuɗi na 2025 mai taken "Kasafin Haɓaka Tattalin Arziki da Rage Talauci an gabatar da shi ga Majalisar dokokin Jihar

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gabatar da jimillar kuɗi N320,811,000,000 a matsayin ƙiyasin kasafin kuɗin shekarar 2025 ga Majalisar Dokokin Jihar.

Wannan Kasafin kuɗi na 2025 mai taken “Kasafin Haɓaka Tattalin Arziki da Rage Talauci an gabatar da shi ga Majalisar dokokin Jihar ranar Alhamis.

Da yake gabatar da kasafin kuɗin, Gwamna Buni, ya ce an gabatar da kimanin Naira  N144,036,787,000 wanda ke wakiltar kashi 44.9 cikin 100, a matsayin kasafin kuɗi na yau da kullum  yayin da aka ware Naira 176,774,213,000 wanda ke wakiltar kashi 55.1 cikin 100 na manyan ayyuka.

Ya ƙara da cewar, kasafin kuɗin shekarar 2024, yanayin yadda aka gudanar da shi na nuna samun nasarar kashi 76 cikin 100 zuwa 30 ga watan Satumba 2024.

A cewarsa a shekarar 2025 gwamnatin jihar ta ƙudiri aniyar gina tituna da gyaran fuska ga wasu domin samar da sauƙin gudanar da harkokin sufuru ga al’ummar Jihar.

Gwamnati ta himmatu wajen ganin an kammala ayyukan tituna 17 da ake gudanarwa, tare da fara wasu sabbin 11, wadda nan ba da daɗewa ba za a fara aikin gina gadar sama a  Damaturu fadar Jihar.

Gwamnan ya ce, za a ƙara haƙar rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana tare da inganta aikin samar da ruwa da sanya sabbin bututun ruwa a garuruwan Damaturu, Buni-Yadi, Nguru, Geidam da Potiskum.

Ya kuma ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta fara aiki a birnin Damaturu na tattalin arziki, da kuma zage damtse wajen gudanar da aikin gyaran cibiyoyin kula da dabbobi na Nasari da Gurjaje da Bade-Gana tare da sayan kayayyakin gudanar da aikin gona.

A nasa jawabin yayin karɓar kasafin kuɗin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Honorabul Chiroma Buba Mashio, ya ce majalisar za ta yi aiki kan kasafin kuɗi domin a gaggauta zartar da shi.