✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zamfara: An cafke mahara a Fadar Sarkin Shinkafi

18 daga cikin mutanen da suka kai hari a gidan basaraken sun shiga hannu

Jami’an tsaro sun cafke mutum 18 da suka kai hari tare da yin barna a Fadar Sarkin Shinkafi, Jihar Zamfara.

Rundunar ’Yan Sandar Jihar Zamfara ta cafke mutanan ne bayan da ta tarwatsa gungun masu tarzoma, dauke da muggan makamai da su ka yi ta barnata dukiyoyi a garin na Shinkafi.

“Matasa dauke da bindigogi da adduna da kuma sanduna sun kai farmaki tare da yin barna a Fadar Sarkin Shinkafi da wasu gidaje biyu a garin

“Cikin gaggawa jami’an ’yan sanda da gwiwar sojoji suka tarwatsa masu zanga-zangar dan guje wa karya doka da oda da kuma asarar rayuka da dukiyoyi.

“Mutum 18 din da ake zargi na hanun ’yan sanda ana binciken su,” inji kakakin ’yan sandar Jihar, Muhammad Shehu

Ya Kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandar Jihar, Abutu Yaro ya ba da umarnin a zurfafa bincike domin gano ummul’haba’isin tarzomar.

A cewarsa, Kwamishinan ’Yan Sandar ya yi kira ga iyaye da su rika lura tare da kwabar ’ya’yansu domin guje wa fadawarsu cikin miyagun ayyuka.