Jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) sun kama mutane 105 da suka haɗa da ’yan ƙasar China huɗu a wata harabar kasuwanci da ke unguwar Gudu a Abuja.
Shugaban sashen yaɗa labarai na EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
- Gwamnan Akwa Ibom ya kori duk Kwamishinoninsa
- Rikicin Masarauta: Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Bayero
“A ci gaba da ƙoƙarin da take yi na tsaftace al’ummar ƙasar daga damfarar intanet da sauran ayyukan cin hanci da rashawa, jami’an Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, (EFCC) sun kama wasu ’yan China huɗu da ‘yan Najeriya 101 a wata harabar kasuwanci da ke unguwar Gudu a Abuja. – cewar Hukumar.
Oyewale ya ce, an kama waɗanda ake zargin ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairu 2025 inda ya ce sun haɗa da maza 67 tare da ’yan ƙasar China da ake zargi da kuma mata 38.
An samu rahoton cewa ana zargin rukunin da wata badaƙalar harkokin duba ayyukan otal da ake yi wa waɗanda suke son damfara da kuma cibiyoyin rukunin wadanda aka kama a Turai da sauran sassan duniya.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa waɗanda ake zargin za su fuskanci hukunci bayan kammala bincike.