✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zamantakewar aure: Dalilin da mata ke neman shawara a kafofin sada zumunta

Wani lamari da ya zamo ruwan dare a yanzu shi ne na yadda wasu mata suka ta’allaka da shafukan sada zumunta wajen neman mafita daga…

Wani lamari da ya zamo ruwan dare a yanzu shi ne na yadda wasu mata suka ta’allaka da shafukan sada zumunta wajen neman mafita daga matsalolin da ke samun su.

Wadannan matan dai kan tura sako  ga masu shafukan, wadanda yawanci mata, su nemi a boye sunansu da salon da a ke kira ‘Hide My ID’, sannan su nemi mafita kan matsalolin da a mafi yawan lokuta na aure ne ko soyayya.

Wata baiwar Allah da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa ta taba neman mafita a wani fitaccen shafin Facebook na Arewacin Najeriya da ake kira da ‘Northern Hibiscus’.

Sai dai ta bayyana cewa maimakon ta samu mafita daga matsalar, sai aka kare da rikita mata lissafi.

Ta ce, “Na taba shiga wata matsananciyar damuwar da ta dimauta ni bayan na ga mijina na hirar batsa da musayar bidiyon banza da matan Facebook.

“Amma madadin a ba ni mafitar da na nema, sai aka hau ni da zagi kan mene ne dalilin da ya sa na binciki wayar mjina har na gano waccan halayyar tasa.

“Wasu kuma sun ba ni shawarwarin cikin lumana, amma saboda mabambanta ne sai na rude.

“Kin san yadda mutane ke daukar zunubin miji ba komai ba, sai na matar da ta gano laifin nasa ta yi magana,” in ji ta.

Wasu Labaran Kirkirar su muke yi —Mai kula da shafin Facebook

Masu kula da irin wadanan shufukan su ke daukar hotunan tambayoyin da matan suka aika musu, su datse sunan wadanda suka aiko, sannan su sanya a shafukan don masu bibiyar su su laluba mafita.

A baya dai ana kiran masu kula da shafukan ‘Admin’, amma a yanzu musamman a Facebook da Instagram, su koma ‘malaman aji’.

Wata mata mai suna Furaira Musa (kirkirarren suna) ta ce a mafi yawan lokuta, su suke kirkirar sakonnin su dora, saboda ‘a motsa dandali’.

“Na farko ya kamata mutane su sani ba kodayaushe suka ga ‘Hide My ID’ din nan ne gaskiya ba, domin akan wayi gari kana da shafi amma ba ka da abin da za ka sanya don motsa shi ka samu karin magoya baya.

“To a nan muke bude wani shafin da suna daban, mu tura sakon kamar mu aka turo wa, sai mu watsa shi ga al’umma.

“Dalili, ba kai kadai ne ke da dandali ba, musamman a Facebook da mutanenmu suka fi yawa, don haka dole ka nemi wani abu da zai ja hankalin mutane su yi magana da kuma yada shafinka; A haka ne za ka samu karin masu bibiya.

“Amma fa ba wai hakan na nufin ba a samun masu turo na gaske ba, wani lokacin a rana daya sai ka samu irin wadannan 10.”

Yin watsai da matsalolin ’ya’ya ke kawo hakan —Masana

Maryam Hassan Baba, ita ce shugabar makarantar Northern Therapist da ke da bada shawarwari kan zamnatakewa ga matasa musamman ma’aurata a Najeriya, ta kuma ce rashin jan ’ya ’ya a jika da kuma maida matsalar auren ’ya’yansu ba komai ba ne ya jawo hakan.

“Yawancin matan nan za ki ga rashin shakuwa da iyaye da ’yan uwa ne ya sa suke fita duniya neman shawarar da a karshe za ta jawo musu zagi.

“Wasu kuma za ki ga saboda sun sha kai wa iyayen kuka kan wata matsala da suke fama da ita a gidan aure ba a magance ba suke yi n haka.

“Iyaye na wani kuskure, na ’yarsu ta kai musu kuka ko korafi kan matsalar aure, madadin su saurare ta, sai su sace mata guiwa su ce ta koma gidan mijinta ta ci gaba da hakuri.

“To daga nan za ki ga ba za ta kara kai musu koken ba, ta gwammace ta je kafar sada zumunta; wasu a kan yi dace su samu shawara  mai kyau da za ta zamar musu mafita, wasu kuma sai dai su sha zagi.

“Su kuma dama masu kafafen nan haka suke so, ba damuwarsu ba ce a samu mafita, su dai kawai a turo su watsa wa duniya, shafukansu su habaka,” in ji ta.

 

Don karanta cikakken rahoton, Ku nemi jaridar mu ta Aminiya ranar Juma’a.