✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamanin razana jami’anmu saboda sakamakon zabe ya wuce —INEC

Sayen Katin Zabe aikin banza ne kawai, in ji INEC.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta yi gargadin ’yan siyasa su kwana da sanin cewa zamanin sace akwatin zabe da razana jami’anta da bindiga don bayyana sakamakon zabe da sauransu, ya wuce.

INEC ta ce da samuwar Dokar Zabe ta 2022, babu sauran wata dama ta tafka magudi yayin zabe.

A cewar Kwamishin INEC, Johnson Alalibo Sinikiem, Sashe na 65 na Dokar, ya bai wa INEC ikon kin amincewa da duk wani sakamakon zabe da aka tilasta wa jami’anta bayyanawa.

“An saukake wa INEC aikinta saboda ba za mu sake shaida satar akwatin zabe ba, sannan zabe zai gudana cikin sauki da albarkacin na’urar BIVAS,” in ji shi.

Da yake jawabi a wajen taron Makon ‘Yan Jarida a Fatakwal, Kwamishinan ya ce INEC za ta yi aiki tare da hukumomin ICPC da EFCC domin yaki da harkar sayen kuri’a a lokacin zabe.

Don haka ya gargadi ’yan siyasar da suka ba da himma wajen sayen katunan zabe da cewa aikin banza kawai suke yi, saboda sayen katin ba zai amfane su ba.