Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya ce Peter Obi ya yi wa Rabiu Musa Kwankwaso nisa a harkar siyasa.
Ahmad, ya yi wannan tsokaci ne bayan da Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa ya girmi Peter Obi a siyasance.
- Da jami’an gwamnati nake zuwa tattaunawa da ’yan bindiga – Gumi
- Dalilin da ba a fara biyan masu hidimar ƙasa N77,000 ba — NYSC
Jagoran na Kwankwasiyya, ya yi wannan furuci ne a wata hira da aka yi da shi a Kano.
Ya ce matsayinsa a siyasa ya fi na Peter Obi, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Labour Party a zaben shekarar da ta gabata.
A martaninsa da ya wallafa a shafinsa na X, Bashiry ya bayyana cewa ko da yake yana girmama Kwankwaso a matsayin ɗan siyasa mai son ci gaba jama’a, amma ba zai yarda da wannan iƙirarinsa ba.
Ahmad ya bayyana: “Ni ba ɗan Kwankwasiyya ba ne, amma koyaushe ina girmama Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan siyasa masu kishin ci gaba da muke da su a ƙasar nan.
“Amma ba zan yarda da iƙirarinsa na cewa ya fi Peter Obi a siyasa ba.
“Idan ka duba sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi ya samu ƙuri’u 6,101,533 kuma ya yi nasara a jihohi 11.
“A ɗaya ɓangaren, Sanata Kwankwaso ya samu ƙuri’u 1,496,687 kuma ya yi nasara ne kawai jiha guda ɗaya, wato Kano.
“Waɗannan alƙaluma sun nuna cewa a zaɓen 2023, Peter Obi ya fi samun tasiri a siyasa a faɗin ƙasar nan.
“Saboda haka, a siyasa, Peter Obi ya fi Kwankwaso tasiri a siyasa.”