✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamana a gidan yari jarabawa ce daga Allah – Farouk Lawan

Lawan, ya bayyana zaman kason da ya yi a gidan yari a matsayin jarabawa daga Ubangiji, wanda ya ce ya koyi muhimman darusa na rayuwa.

Tsohon Ɗan Majalisar Wakilai, Farouk Lawan, ya kai ziyararsa ta farko mazaɓarsa ta Bagwai da Shanono tun bayan fitowarsa daga gidan yari.

Lawan, ya bayyana zaman kason da ya yi a gidan yari a matsayin jarabawa daga Ubangiji, wanda ya ce ya koyi muhimman darusa na rayuwa.

Idan za a tuna, an yanke masa hukunci a shekarar 2021 saboda karɓar cin hancin Dala dubu 500 daga hannun hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Mista Femi Otedola, mai kamfanin mai na Zenon Oil.

Lamarin ya faru ne yayin binciken tallafin man fetur a shekarar 2012, sai sai ya kammala zaman ɗaurin shekaru biyar a gidan yarin Kuje a watan Oktoban 2024.

A ziyarar da ya kai garin Bagwai, inda ya samu tarba daga ’yan Kwankwasiyya, Hakimin gundumar, Alhaji Nura Shehu Ahmed, ya yaba da yadda yake ɗan siyasar da ke son tallafa wa al’umma duk da cewa yana tsare.

Ya samu rakiyar magoya bayansa, inda ya jaddada cewa ziyarar tasa ba ta siyasa ba ce, sai dai don nuna godiya ga yadda al’umma suka nuna masa ƙauna da kuma nuna baƙin cikinsu kan mawuyacin halin da ya tsinci kansa.

Ya kuma bayyana abin da ya same shi a matsayin jarabawa daga Allah, inda ya kwatanta da labarin Annabi Yusuf, wanda ya yi fice bayan ɗaure shi.

Tsohon ɗan majalisar ya kuma kai ziyarar ta’aziyya a sassan ƙananan Hukumomin Bagwai da Shanono, ciki har da fadar Hakimin Shanono, Alhaji Ibrahim Sani Gaya.

Duk da dagewar Lawan cewa ziyarar ba ta siyasa ba ce, amma ra’ayoyi kan makomar siyasarsa sun rabu.

Alhaji Saidu Sarkin Ya, mazaunin yankin kuma ɗan jam’iyyar NNPP, ya yi imanin cewa Lawan zai iya lashe kowane zaɓe idan ya ga dama, duk da cewa zai buƙaci afuwar shugaban ƙasa.

Sarkin, ya yi hasashen cewa jam’iyyar APC za ta yi zawarcin tsohon ɗan majalisar ya dawo cikinta, matakin da yake ganin zai iya shafar farin jininsa.

Sai dai a cewar Alhaji Garba Sani Bagwai, magoya bayan Lawan za su bi shi, duk jam’iyyar da ya je ba tare da la’akari da siyasarsa ba.

Idan za a tuna  zaɓen 2025 tsohon ɗan majalisar da ke a matsayinsa na ɗan takarar Jam’iyyar PDP ya sha kaye a hannu jam’iyyar APC.

A wannan ziyarar da ya kai a baya-bayan nan, ya samu rakiyar masu riƙe da muƙamai da magoya bayan NNPP, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan yadda zai tafiyar da harkokin siyasarsa a halin yanzu.