Wasu matuka ababen hawa a garin Gombe sun koka kan yadda masu gidajen mai suke rufe gidajensu da nufin kara kudin man fetur.
A ’yan kwanakin nan dai matsalar wahalar man ta yi kamari a birane da dama ma Najeriya, lamarin da ya ’yan bumburutu ke cin karensu ba babbaka.
- An kama mabaraciya da tsabar kudi sama da N500,000 a Abuja
- Kotu ta daure matan aure 2 a Kaduna saboda cizon juna
Wani mai sanar acaba a garin Gombe, Haruna Danjuma, da wakilinmu ya zanta da shi ya yi zargin cewa mafi yawancin ’yan kasuwar man ne suke ta kokarin ganin an kara farashinsa don ya yi tsada shi yasa suke kulle gidajensu suna kin sayarwa.
Danjuma ya ce suna sayar wa ’yan bumburutu ne kawai a jarkuna ba masu ababen hawa ba, wanda hakan ya sa mai baya samuwa a gidajen man, sai a wajen ’yan bunburutun.
Kazalika, shi ma wani direban mota da muka tuntuba mai suna Abbas Salisu, ya ce wahalar man ta sa suna daukar fasinja a kan faduwa, saboda kudin mota bai karu ba, amma kudin mai a kasuwar bayan fage ya karu kadan.
Wani mai sana’ar bumburutu a gefen hanya, Yakubu Halliru, ya ce suna samun man ne daga gidajen mai, amma duk jarka daya da aka cika musu suna bayar da N200 lamarin da ya sa suke sayar da lita a kan N270 maimakon N250.
Yakubu Halliru, ya ce yanzu da man yake dan wahalar samuwa suna samun kasuwa fiye da a baya domin idan mutum ya rasa mai a gidan mai dole a wajensu zai saya, su kuma suna dan kara kudi don su samu riba saboda yadda suke ba da kudi kafin a basu.
Wakilinmu ya yi kokarin dan jin ta bakin Shugabann Kungiyar Dillalan Mai ta IPMAN, amma amma hakarsa ta gaza cimma ruwa.