Fitaccen dan siyasa kuma Dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya ce rashin adalci a ce wani mutum daga yankin Arewacin Najeriya ya fito neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023.
Tanko Yakasai ya ce zalunci ne yankin Arewa ya nemi takarar shugaban kasa alhali yankin Kudu na ta korafi tare da neman samun damar tsayar da shugaban kasa bayan karewar wa’adin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a 2023.
- Kisan Hanifa dabbanci da rashin imani ne —Atiku
- Najeriya: Matsala jiya, matsala yau kuma matsala gobe?
Kalaman nasa na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da zazzafar mahawara tsakanin masu ruwa da tsaki a siyasa a Najeriya game da yankin da za a ba wa takarar shugaban kasar a zaben na 2023, tsakanin Arewa da Kudu.
Tuni dai wasu ’yan Arewa sauka fara zawarscin kujerar, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwanman Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon Gwamnan Jihar Kwara Sanata Abubakar Bukola Saraki da kuma Gwamnan Jihar Sakkwato mai ci, Aminu Waziri Tambuwal.
Alhaji Tanko Yakasai, wanda ya ce a halin yanzu shi ba dan wata jam’iyya ba ne, ya jaddada cewa shi dan siyasa ne da ya yi amannar cewa rashin adalci ga yankin Kudu idan har dan Arewa ya zama magajin Shugaba Buhari a 2023.
Ya ce, “Ta yaya za a yi a ce ’yan Arewa ne kadai za su yi mulki? Ai wannan zalunci ne. Adalci shi ne mu (Arewa) mu yi mulki, su ma (Kudu) su yi.
“Duk da cewa ba mu tabuka abin a zo a gani ba a tsawon lokacin da ’yan Arewa suka yi mulki, me za mu ce wa mutane?
“Me ma za mu nuna wa ’yan Najeriya da suka ci gajiya da har za su jefa mana kuri’arsu? A tsawon shekara shida zuwa bakwai da suka gabata me muka yi?
“Wace nasara muka samu da ta kawo wa kasar nan cigaba ta fuskar tattalin arziki ko wani ci gaba da ya taimaka wa jama’ar kasa?
“Da wace nasara za mu iya amfani mu ja ra’ayin mutanen Najeriya su sake ba mu kuri’arsu? Sabdoa haka ni a ra’ayina, idan Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa, ’yan Arewa su hakura.
“Nan gaba zai kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas, to me zai sa wani dan Arewa ya sake tsayawa takara shi ma ya yi shekara takwas, tun da kowannensu yana da damar yin wa’adi biyu. Gaskiya babu adalci,” inji Alhaji Tanko Yakasai.
Ya bayyana cewa tun farko abin da ya fi damun shi a siyasa shi ne yin adalci, yana mai bayani cewa ya goyin bayan takarar tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a zaben 2015 ne, “Saboda ina son tabbatar da ganin an bar kowane Shugaban Kasa ya yi wa’adin mulkinsa na biyu bayan ya yi na farkon.
“Idan shekara hudunsa na farko ba su ishe shi ya cim-ma muradunsa ba, shekara takwas suna da tsawon da za su ishe shi ya tsara yadda zai kammala su,” inji Alhaji Tanko Yakasai.
Game da mau hankoron takarar shugaban kasa a zaben 2023, Tanko Yakasai ya ce jagoran jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ne mutumin da ya fi cancanta idan aka yi la’akari da tarihin da ya kafa wajen kawo wa Jihar Legas ci gaba.