Sanata Kabiru Marafa tsohon Dan Majalisar mai wakilai Zamfara ta Tsakiya na tsawon zango biyu a Majlisar Dattawa ta Najeriya.
A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana abubuwan da ya hango tun wancan lokaci da ya yi ta magana a kan harkokin tsaro a Arewa maso Yamma da takun sakarsa da Gwamnan Zamfara na wancan lokacin, Abdulaziz Yari wanda har ya kai APC ta rasa jihar baki daya.
Yaya rayuwa tun bayan barin Majalisar Dattawa?
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai. Rayuwa tun bayan zaben 2019 sai godiya ga Allah.
Daga kallo za ka ga na kara fari da kiba kuma hankalina a kwance.
Idan aka zabe ka nauyi aka dora maka. Duk ranar da Allah Ya nuna maka ka sauke wannan nauyi lafiya, babu abin da ya kamata face godiya ga Allah.
Duba da inda aka faro zuwa yanzu, ni sai godiya ga Allah kawai.
Kuma na taka rawa wadda ni kaina lokacin da zan shiga ban taba tunanin zan yi kashi daya cikin dari ba. Allah Ya ba ni cikakkiyar nasara.
Kun samu takun saka da tsohon Gwamnan Abdulaziz Yari, yaya alakarku yanzu?
Abin da ke tsakanina da Abdulaziz Yari ba kiyayya ba ce ko gaba.
Abin da ya faru na siyasa ne. Shi yana ganin abubuwa yadda yake ganinsu, ni ina gani yadda nake gani.
Shi yana gani a wancan lokaci bai kamata in kara taka wata rawa ba a siyasa, ni kuma ina ganin wani dan Adam bai isa ba ya ce wani dan Adam ga yadda zai yi.
Mun hadu ne a shekarar 2011. Ba gidan siyasa daya muka fito ba. Sun samu baraka a jam’iyyarsu da shi da su Mamuda Shinkafi gwamnan wancan lokaci. Ni ma na samu baraka a namu gida na PDP inda shi Shinkafi ya dawo.
Sai Allah Ya hada mu kuma Ya biya wa kowa bukatarsa. Sai shi a cikin hikimarsa ta shugabanci, ya ga bai kamata in sake komawa Sanata ba ko ma in yi takara.
Ni kuma na ga gaskiya bai isa ya fada min haka ba. Don haka na nemi hakkina.
Wannan ya kai mu ga abubuwa da suka faru har muka kai Kotun Koli daga karshe Allah Ya yi ikonSa.
Ni a wajena wannan matsalar ta kai karshe. Wadda ta rage ita ce ta jayayya a kan shugabancin APC a Zamfara.
Amma dai ni ba ni da wata takamammiyar matsala da wani dan siyasa. Idan muka hadu da Abdulaziz Yari, tafawa muke yi sosai ba wai gaisawa kawai ba.
Ina so jama’a su gane cewa abin da na yi bai saba wa addini da al’ada ba.
Kariyar kai na yi. Babu inda aka ce a addinin Musuluci mutum ya zo kashe ka, ka mika wuya kawai ya kashe ka domin inda ya fito su zauna lafiya.
Cewa za ka iya kare kanka. Wancan matsala shi Yari ne ya haifar da ita. Do haka yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Idan yana so mu ci gaba da jayayya ko ya isa haka to. Ko kuma ita uwar jam’iyya ta duba ta ga abin da ya fi dacewa.
Akwai rade-radin kana goyon bayan PDP a Zamfara, me za ka ce?
Ka san an ce makiyinka ba ya ganin kwazonka. Ba maganar PDP za a ba. Ni ina goyon bayan duk abin da zai kawo wa mutanen Zamfara masalaha da ci gaba da kwanciyar hankali.
Ai siyasa ba addini ba ce. Da PDP da APC babu wadda aka ce sai an yi kalmar shahada za ka shiga. Don haka, yadda ka shiga kana iya fita.
Abin da zai canza shi ne kawai mutuncinka idan ka cika zagaye-zagaye a ce ko dogon buri kake da shi. Amma babu wanda zai ce ka yi ridda.
Ka kaddara ma ban taka wata rawa a zamowar gwamnatin ba, duk gwamnatin da za ta zo ta taimaka wa mutanen Zamfara, musamman a irin halin da Zamfarawa suka shiga da irin gwagwarmaryar da muka yi, to zan goya mata baya.
Ni na san halin da mutanen Zamfara suke ciki. Don haka idan gwamnatin yanzu za ta ci gaba da yin abin da take yi na samar wa Zamfarwa masalaha, to lallai ni Kabiru Marafa goyon baya yanzu na fara.
Abin da za a ce kawai shi ne idan kana hada baki da gwamnati ana cutar da mutanen Zamfara ko kana kwashe musu wani abu.
Ke nan ka yi amanna da ayyukan gwamnatin?
Idan ka ce amanna, dole za a fassara abin. Lokacin da gwamnatin ta cika shekara, a wannan rana, wasu mutane sun dauki nauyin talla a Daily Trust cewa an kashe ina tunanin mutum 387 a shekara daya.
Su suna ganin sun yi haka ne domin su yi batanaci, amma ni a ganina duk da cewa duk yaruwar mutum na da muhimmanci, sai na kalli abin cewa ita gwamnatin ta yanzu kamata ya yi ta yi alfahari.
Mun yi lokacin da a rana daya cikin awa 2 an kashe mutum 387 a kuaye daya. Amma sai aka ce yanzu an kashe 387 a shekara daya.
Abun bai da dadi, domin su ma mutane ne, amma la’akari da inda aka fito da inda ake yanzu, to lallai an samu sauki.
To batun yin amanna, daga abin da nake ji daga mutane har da ’yan adawa, ni ba gwamnati nake sauraro ba, amma an samu ci gaba a harkokin na tsaro, wanda kuma shi muke fata ko ma waye zai yi gwamnati. Abin da ake bukata shi ne mu ci gaba da ba su goyon baya kuma mu ci gaba da addu’a a gare su.
Me za ka ce kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Yamma?
Ni ba ma’aikacin tsaro ba ne, kuma ban yi aiki da hukomomin tsaro ba. Amma abu daya da na sani shi ne an yi sakaci.
Daya daga cikin abubuwan da suka haifar mana da matsala da Gwamna Yari a wancan lokaci ke nan.
Shi a ganinshi, bai kamata a yayata matsalar ba domin yana gani kamar kasawa ce a gare shi, ni kuma ina gani akwai bukata domin idan ba ka fada ba, babu wanda zai sani ballatanta a kawo dauki.
Yanzu gidanka ana yunwa, idan ba ka fada wa makwabcinka ba, ba dole ba ne ya sani har ya kawo dauki.
Abu na biyu babbar matsalar ita ce ta masu kai labari ga ’yan bindiga.
Kuma wadannan mutane ’yan uwanmu ne tare muke zama da su. Dole sai dukkanmu mun gane cewa wannan matsalar ta mu cewa baki daya.
Sannan uwa uba ita ce ta cin hanci da rashawa ko kuma zalunci. Muddin ba za a daina zalunci ba wajen gudanar da al’amura na jama’a, mastaloli ba za su kare ba.
Abin da ake ba muhimmanci a da shi ne mutunci, amma yanzu kudi ne. Yanzu ba ka da girma, ba a girmama ka sai kana da kudi. Kuma babu wanda ya damu daga ina aka samu kudin.
A da Mai Unguwa ba Uban Kasa ko Hakimi ba, darajar da yake da ita idan ya kira Sarkin Fulani ya ce me ya sa aka yi kaza da kaza, za ka ga an samu masalaha, amma yanzu sarakunan ba su iya fada a ji kamar da.
Ya kamata a dawo a ba kowa darajar da ya kamata. Dole mu dawo mu gane cewa wannan halin da muke ciki na bin kudi babu inda za ta kai mu sai ga halaka.
Kana ganin sulhu da ake yi da ’yan bindiga zai haifar da da mai ido?
A tunanina mai daki shi ya san inda ruwa ke zuba. Don haka wanda ya ga sulhu zai yi masa aiki, ya rumgume shi ya yi, mutane su taya shi da addu’a, wanda ya ga akasan hakan zai yi, shi ma haka domin yana da dalili. Kowa ya tsarkake zuciya.
Mu kuma mu taya su da addu’a, sannan mu duba, idan mun ga ba ya yi ne, sai mu yi magana mu ce wane abu kaza da ka sa a gaba ba ya yi. Ni dai ina goyon bayan duk abin da zai kawo maslaha.
Lokacin kana majalisa, ka kawo kuduri inda har aka fitar da Naira biliyan 10 ga mutanen Zamfara karkashin shirin Presidential Initiatibe of Zamfara State (PIZAMS), ina aka kwana kan batun?
Gaskiya ban so in alakanta abin da wani ya yi laifi, amma maganar gaskiya wadanda suka gaje mu ba su taka rawa ba a kan maganar.
Babu abin da aka yi, batun kudin ya lalace, ba a karbi ko Naira daya ba, kwamitin da muka ce a kafa, majalisa ta amince kuma aka kai wa Shugaban Kasa babu abin da aka yi har yau. Wannan gaskiya abin bakin ciki ne, kuma ban ji dadi ba.
Da Gwamnan Zamfara ya fara magana, amma maganar gaskiya ba maganarsa ba ce. Maganar sanatoci da ’yan majalisa domin majalisa ce ta yi kudurin. Don haka su ya kamata su bi wannan abu.
Kuma ai ba Naira biliyan goma ba ne, na farko ne aka ba da biliyan 10, abin da na nema shi ne a kafa wannan hukuna na tsawon shekara 10, kuma duk shekara a sa kudi a wannan hukuma.
To da sun bi, watakila shekarar da ta biyo a samu sama da biliyan 10.
Amma a musu adalci watakila sun yi abin ya fi karfinsu. Amma ya kamata mutanen Zamfara su musu tambaya su kare kansu.
Matsalar da ke kwance a irinsu Sokoto da Kastina da Zamfara, idan suka taso za a sha mamaki. Ba a tunanin matan da aka kashe wa maza da yaran da suka zama marayu.
Amma wata rana za a musu tambaya a kan cewa wata rana an yi wani abu kaza me ya faru daga nan babu wanda ya bi.
Kuma zan yi kira ga Shugaban Kasa da ya duba wannan al’amari, a kafa wannan hukuma domin a taimaka wa muatenmu ko da ’yan majalisa sun yi wani abu ko ba su yi ba.
Shin kana tunanin APC ta sauke nauyin da ta dauka?
Ba na shiga layin wani. Amma in ma dai an cika alkawuran ko ba a cika ba, ina rokon Shugaban Kasa ya duba mana hanyar Abuja zuwa Kano da Zariya zuwa Funtua, sannan a duba harkokin tsaro a yankunanmu.
Ana batun APC za ta mayar da mulki Kudu, inda wasu ke cewa APC za ta iya watsewa?
Komai yana da lokaci. Yanzu lokaci ne na gudanar da mulki, ba siyasa ba. Amma kafin lokacin ya yi ya kamata mu ji tsoron Allah.
Abin da yake ci mana tuwo a kwarya shi ne zaluntar kai ko munafurci. Shin ita Najeriya tsagi biyu ce ko yankunan mulki shida? Dole a duba wannan kafin 2023.
Idan biyu ne, sai a ce Arewa ta yi saura Kudu, in shida ne akwai matsala ke nan. Sai a duba inda ya yi, abin da zai yi wahala shi ne a samu daga Arewa maso Yamma ke nan.
Mene ne shirinka na zaben 2023?
Ina ganin ya yi sammako a fara maganar nan yanzu domin yanzu rayuwa babu tabbas na ganin gobe ballantana shekara uku.
Abin da zan ce shi ne ban yi riyata ba, ban bar siyasa ba.
Amma abubuwan da za su gudana ne za su nuna min abin da ya kamata in yi. Amma maslahar mutanena ne a farko.
Ganin kuna da sabani a Jam’iyyar APC a Zamfara, za ku gyara ku dunkule kafin lokacin?
Yanzu ai rikicin ya tashi daga jihohi ya kawo tsakiya, wanda ya kai har aka rushe tsakiyar aka kafa kwamiti karkashin Gwamna Mai Mala Buni.
Ina masa fatan alheri, kuma ya yi sakataren jam’iyya, ina ganin ya san asalin matsalar, kuma ina ganin za su yi abin da ya kamata. Ina kyautata zaton za su iya dinke matsalar rikicin Zamfara.
Tun lokacinku ake samun takun saka tsakanin Majalisar Dokoki da bangaren zartaswa, me ke kawo hakan ganin cewa kwanan an samu musayar yawu tsakanin ’yan majalisa da Minista a Ma’aikatar Kwadago Festus Keyamo?
Akwai karin magana da ake cewa suzuki lafiyarka hayaki.
To haka lafiyar mutanen kasa a rika samun takun saka a tsakanin Majalisar Dokoki da Zartarwa, amma ba mai yawa ba.
Duk lokacin da ka ji shiru, to mutane na cutuwa domin akwai hadin baki. Don haka takun saka ba wani ba ne sabo.
Amma barakar da aka samu wajen batun daukar ma’aikata tsakanin majalisar da Festus Keyamo, shi Keyamo ya gode wa Allah ba irinumu ba ne a majalisa domin shi ne bai da gaskiya.
Misali kwamitin da ya kafa a Zamfara na daukar ma’aikatan, mutanen mutum daya kawai ya dauka. Ko ba ka san mutanen Zamfara ka san akwai minista da tsohon gwamna Yari da ni da sauranu.
To da wa ya yi sharawa wajen kafa kwamiti, to shi dan Zamfara ne?
An wayi gari da batun nada Femi Fani Kayode Sadaukin Shinkafi, me ka za ce a matsayinka na dan Zamfara?
Abin alfahari ne wannan tunda mun ce Najeriya kasarmu ce baki daya.
Komai yana da sila, ban san wa kai shi ba, amma dukkansu sun cancanci yabo domin wani abu ne zai kara dankon zumunci domin kasancewarsa Bayarabe ya je Zamfara garin Hausawa da Fulani an ba shi sarauta. Don haka ina ganin abu ne mai kyau.