Barkanmu da warhaka Manyan gobe ya ya karatu? Tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Zaki da Dila’. Labarin ya yi nuni ga illar rashin godiya. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
Akwai wani Zaki a wani daji. Zakin ya kasance shi ne sarkin dabbobi a dajin. Ran nan ya fita neman abinci sai wani sartse ya shige masa hannu. Ya fi wajen awa daya yana kokarin fitar da sartsen a hannunsa amma abin ya ki.
Sai ya kira dabbobi su taimaka masa amma babu wanda ya je ya taimaka masa saboda sanin halinsa na mugunta.
Can sai Dila ya ce zai taimaka masa, amma yana da sharadi. Sai Zaki ya tambaye shi sharadin? Sai ya ce sai ya naushe shi sau biyar. Abin ya bata wa Zaki rai, amma saboda tsananin zafin da yake ji sai ya ce ya yarda, amma a cikin zuciyarsa ya yi alkawarin sai ya rama dukan da Dila ya masa.
Dila ya kira Bushiya ta zo ta cire wa zaki sartsen da ya addabe shi. Zaki yana son ya rama abin da Dila ya yi masa a kan Bushiya. Koda ya kai fuskarsa kan Bushiya, sai Bushiya ta harbe shi da kibiyarta wanda hakan ya sanya Zaki ya yi da na sanin aikata haka.
Tare da fatan Manyan gobe za su zama masu yawan yafiya a duk lokacin da aka saba musu.