✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zakarun Turai: Yadda Juventus ta shiga da kyar

Juventus ta samu shiga gasar Zakarun Turai ta 2022 bayan ta yi wa Bologna 4 - 1.

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta 2022 da kyar bayan da ta lallasa kungiyar Bologna da ci 4 – 1.

Sai dai a tsakiyar wasan, duk da cewa Juventus din na lallasa Bologna, ’yan wasan ba sa murna kasancewar kungiyar Napoli da AC Milan ma suna cin wasanninsu.

Sai dai daga baya kungiyar Hellas Verona ta farke kwallo daya da Napolin ke cin ta, inda aka tashi kunnen doki, wanda hakan ya sa Juventus din ta samu gurbin shiga.

Ko da aka tashi wasan, Juventus ta kasa sakin jikinta, sai da ta jira aka tashi wasan na Napoli kafin hankalinta ya kwanta.

Kafin kakar bana, Juventus ta lashe gasar Serie A sau tara jere, inda a farkon kakar aka rika tsammanin za ta lashe ta 10.

Amma kuma kungiyar Inter Milan ce ta lashe gasar bayan abubuwa sun juya wa Juventus din baya.

Wani abin mamaki shi ne yadda duk da cewa Juventus din na bukatar lashe wasan na karshe, sai aka ga Cristiano Ronaldo a benci, wanda hakan ya haifar da zullumi.

Sai dai bayan wasan, kocin kungiyar, Pirlo ya ce an hutar da dan wasan ne kawai amma babu wata matsala.