✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zainab Shinkafi-Bagudu: Jagorar yaki da kansa a Afirka

Dokta Zainab Shinkafi-Bagudu na cikin mutanen da suke kan gaba a yaki da kansa

A wannan zamanin, sunan Dokta Zainab Shinkafi-Bagudu ya yi tambari ba kawai a Najeriya ba, har ma a nahiyar Afirka, saboda jajircewarta wajen yaki da cutar kansa ko sankara.

Kamar yadda kwamandan yaki ke bukatar rundunar sojoji, ita ma Dokta Zainab ta kafa Gidauniyar Yaki da Kansa ta Medicaid (Medicaid Cancer Foundation) a Turance don yakar wannan cuta.

A shekara biyar da suka wuce kuma Gidauniyar ta tara sama da N120m don wannan yaki.

Gidauniyar kan wayar da kan al’umma game da cutar kansa, takan horar da ma’aikatan lafiya a kan yadda za su kula da masu larurar, sannan kuma takan biya wa marasa lafiya kudin magani ko aiki.

Bayan yaki da kansa, gidauniyar takan kuma dauki nauyin karatun dalibai masu koyan aikin jinya – misali a shekarar karatu ta 2020/2021 ta dauki nauyin dalibai mata 40 daga jihohin Kebbi da Sakkwato da Zamfara don su yi karatu a Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Jihar Kebbi.

Daga yakar cututtukan yara zuwa yaki da kansa

Saboda jajircewarta wajen yaki da cutar kansa, Dokta Zainab Shinkafi-Bagudu ta kuma zama mace ta farko daga Afirka, a matsayin mamba a hukumar daraktocin Hadakar Kungiyoyi Masu Yaki da Kansa ta Duniya (UICC), kuma a yanzu haka tana wa’adinta na biyu ne.

Wani abin dubawa game da Tauraruwar tamu ta yau shi ne ba ma a bangaren kula da masu cutar kansa ta kware ba a farkon karatunta na likitanci.

Dokta Zainab liktar yara ce, amma sau da yawa idan mata sun kawo yaransu wurinta sukan shaida mata matsalolin da su kuma suke damun su.

Sai ta lura larurar kansa ta fi yawa a cikin wadannan matsaloli don haka ta fara bincike a wannan bangaren har ta kware, sannan ta shiga yaki da cutar gadan-gadan.

Dokta Zainab Shinkafi-Bagudu dai ta yi karatunta na digiri na farko a bangaren likitanci ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, sannan ta samu kwarewa a bangaren cututtukan yara a Birtaniya.

Bayan dawowarta gida Najeriya, sai ta rika fuskantar kalubale wajen samun sakamakon da take bukata idan ta bukaci a yi wa marasa lafiya gwaji.

Tallafa wa mata

Wannan ya sa ta bude dakin bincike na Medicaid Medicaid Radio-Diagnostics – dakin bincike irinsa na farko – a Abuja a 2009.

Bugu da kari, a matsayinta na Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Tauraruwar ta taimaka wajen assasa shirye-shirye na tallafa wa mata ta fuskar ilimi da sana’o’i.

Ta kuma taimaka wajen ganin Majalisar Dokoki ta Jihar Kebbi ta amince da Dokar Haramtar Cin Zarafin Mutane, musamman don kare hakkokin mata da kananan yara.

Dokta Zainab ta samu lambobin yabo da dama saboda ayyukanta wadanda suka hada da Lambar Yabo ta Kungiyar Likitoci ta Kasa (NMA) a 2018; da Kyautar Fitacciyar Mai Bayar da Gudunmawa ga Kiwon Lafiyar Mata da Yaran Afirka ta London Political Summit & Awards a 2021; da Takardar Shaidar Aikatan Abin A-zo-a-gani ta Majalisar Dokokin Amurka; da wasu da dama.

Mai fafutuka

Tauraruwar marubuciya ce wacce ta wallafa makaloli na kimiyya da wasunsu da dama, kuma fasihiya ce da ta gabatar da jawabai a wuraren tarurruka da dama.

Bugu da kari mamba ce a kungiyoyin al’umma da dama. Ga kadan daga ciki:

Ita ce Shugabar Kungiyar Matan Gwamnoni Masu Yaki da Kansa;

Mamba ce a Hukumar Daraktocin Gidauniyar Mata Masu Fuskantar Hadari ta Duniya (WARIF);

Mamba ce a Hukumar Daraktocin Kungiyar Mata Masu Da’awah a Najeriya;

Uwar Kungiya ce ga Majalisar Kungiyoyin Mata ta Najeriya (NCWS);

Uwar Kungiya ce ga Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya;

Uwar Kungiya ce ga Kwamitin Shirya Gasar Olympics na Najeriya; da sauransu.