A ranar Laraba ce za a fafata wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila da FC Porto da Portugal a wasan dab da na kusa da na karshe na Gasar Zakarun Turai.
Sai dai hankalin masoya kwallon kafa a Najeriya ya karkata kan dan wasan Najeriya daya da ya rage a gasar, Zaidu Sanusi.
Zaidu dan asalin Jihar Kebbi ne da ke Arewacin Najeriya, wanda FC Porto ta sayo daga kungiyar Santa Clara a farkon kakar bana.
Ya buga dukkannin wasannin da kungiyar ta buga a Gasar Zakarun Turai, inda ya zura kwallo daya a wasansu da Marseile.
Dan wasan ya fi nuna kwarewa a wasansu da kungiyar Juventus, inda ya hana Cristiano Ronaldo sakat, sannan yakan samu dama ya je gaba ya taimaka wa ’yan wasansu na gaba.
An haife shi a garin Jega, a ranar 13 ga Yunin 1997, yanzu yana da kimanin shekara 23 ke nan.
A yanzu dai shi kadai ne dan Najeriya da ya rage a gasar ta Champions League.