Dan takarar Gwamnan Jihar Legas a jam’iyyar PDP, Olajide Adediran, ya ce zabar ‘yar wasan kwaikwayo a masana’antar Nollywood Funke Akindele, a matsayin Mataimakiyarsa zai taimaka ainun wajen samun nasarar jam’iyyar.
Da yake tabbatar da ita a matsayin abokiyar takararsa a shafinsa na Twitter ranar Talata, dan takarar ya yi kira ga mazauna jihar da su hada hannu da shi da kuma mataimakiyar tasa domin ciyar da jihar gaba.
- ’Yan wasa 10 da ke takarar gwarzon dan kwallon Afirka na 2022
- Hadarin mota ya yi ajalin mutum 4 a hanyar Legas
Ya kuma ce a shirye yake domin tafiya tare da dukkan wadanda suka nemi kujerar tare da shi, tun daga yakin neman zabe har zuwa lokacin da za su karbi gwamnati a 2023.
“Ga dukkan mazauna jiharmu musamman ‘ya’yan jam’iyarmu ta PDP, ina matukar godiya a gareku kan yadda kuka amince kuka bani wannan tikitin, na yi alkawarin yin iya karfina domin ganin na farfado da jiharmu daga masassarar da makiyanta suka jefa ta.
“Wannan tafiya tamu na bukatar mayar da hankali, juriya da jajircewa. Kuma abokiyar takarata mai kyakykyawar zuciya ce, da dadadden tarihin hidima da gwagwarmaya. Haifaffiyar Ikorodu ce, da nasararta ta yadu ta hanyar ayyukanta da suka inganta yankinmu,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Ina alfaharin gabatar muku da Barista Olufunke Ayotunde Akindele a matsayin Mataimakiyata a zaben 2023 mai zuwa. Tare, za mu hidimta muku da kuma samar muku ci gaban da za ku yi alfahari da shi.”
Funke dai ta tabbatar da amincewa ta zama abokiyar takarar tasa a cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram a safiyar Talata, inda ta ce za ta dakatar da fitowa a wasan kwaikwayo domin mayar da hankali kan yakin neman zaben da take fatan za su yi nasara a jihar ta Legas.