✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben shugabannin APC: Tsintsiya na iya watsewa

APC na fuskantar barazanar tarwatsewa bayan wasu ’ya’yan sun fusata.

Zabubbukan shugabannin Jam’iyyar APC mai mulki a matakan jihohi sun bar baya da kura, inda jam’iyyar take fuskantar barazanar tarwatsewa sakamakon matakan da fusatattun ’ya’yan jam’iyyar da aka bata wa rai a zabubbukan suke kokarin dauka.

Yayin da zaben kasa na shekarar 2023 ke gabatowa, gwamnoni da ministoci da sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai sun ja daga kowanensu ya tashi haikan don nadawa ko dora shugabannin jam’iyyar a jihohinsu.

Rikicin cikin-gida na Jam’iyyar APC ya kara fitowa fili ne bayan zaben sababbin mambobin kwamitin zartarwa inda aka samu tagwayen zabubbuka a kusan kowace jiha, inda fusatattun ’ya’yan jam’iyyar suka shirya nasu zaben na daban.

Wasu jihohin sun gudanar da zaben ne ta hanyar sasanci, yayin da wasu jihohin da jam’iyyar ke da karfi suka yi tagwayen zabubbuka.

Sai dai matakin da shugabannin jam’iyyar na kasa suka dauka na yin fatali da zaben da bangaren fusatattun suka yi, wanda suka ce hakan ya saba wa tsarin jam’iyyar, ya dadada wa gwamnoninta domin sun samu damar mike kafafunsu yadda suka ga dama.

A wata takadar sanarwar da Kwamitin Rikon Jam’iyyar ya fitar ta hannun Sakatarenta, Sanata John James Akpanudoedehe, ta ce za ta yi amfani ne kawai da zaben da rantsattsun shugabannin kwamitin zaben jam’iyyar da aka nada a kowace jiha kuma jam’iyyar ta san da zamansu.

An gudanar da tagwayen zabubbuka a jihohin Kano da Legas da Ogun da Kwara da Osun da Filato da Neja da Akwa Ibom da kuma Enugu, inda wadansu jigajigan jam’iyyar suka ki halartar wurin zaben saboda yadda wadansu gwamnoni suka mamaye zabubbukan, kamar yadda Aminiya ta gano.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau da takwarorinsa na jihohi Ogun; Ibikunle Amosun na Osun; Rauf Aregbesola da Rochas Okorocha na Imo suna cikin wadanda abin ya shafa, kamar yadda ruwa ya bugi Ministan Labarai da Al’adu; Alhaji Lai Mohammed da Sanata Barau Jibril (APC, Kano) da Sanata Godswill Akpabio da sauransu.

Bangaren Aregbesola ya nufi kotu

Damuwa da yadda al’amura suke tafiya, bangaren Minsitan Cikin Gida, Alhaji Rauf Aregbesola, sun kai jam’iyyar kotu bisa abin da suka ce an yi musu na rashin kyautawa.

Karon-batta a tsakanin Aregbesola da wanda ya gaje shi Gwamnan Jihar Osun, Mista Adegboyega Oyetola, sun dagula wa jam’iyyar lissafi a jihar, inda hakan ya sa suka gudanar da tagwayen zabubbuka.

Masu shirin kai karar, sun hada da Yusuf Asifat Makanjuola da wadansu mutum 2,516 ’ya’yan Kungiyar Osun Progressibes (TOP), da suke biyayya ga Aregbesola, inda suka yi korafin cewa sun kashe makudan kudi wajen sayen fom na takarar mukamai a jam’iyyar amma aka yi watsi da su.

A cikin takaradar karar sun shigar da jam’iyyar ta APC, reshen Jihar Osun da Hukumar INEC da Shugaban Kwamitin Sauraron Koke-Koke na Kwamitin Zaben Gundumomi, Ambasada Obed Wadzani, a matsayin wadanda ake kara.

Da yake jawabi game da lamarin, Shugaban Bangaren Aregbesola, Alhaji Rasak Salinsile, ya ce sun zabi daukar mataki na shari’a ne don bi musu kadinsu.

“A yanzu haka mun shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Oshogbo inda muke bukatar a soke hatta zaben shugabannin jam’iyyar na gundumomi da aka gudanar,” inji shi.

Da aka tuna masa rokon da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga ’ya’yan jam’iyyar na su guji kai jam’iyyar kotu, Rasak, ya ce an katse hannuwansu daga duk abin da ya shafi harkokin jam’iyyarsu na cikin gida.

“Babu wata doka a cikin jam’iyyar da ta hana zuwa kotu. Ta ce ne kada mu je kotu har sai mun bi dukkan hanyoyin da suka dace na cikin gida kuma mun yi abin da ya dace.”

Mu ne halattattun shugabanni ba zaben bayan-fage muka yi ba – Bangaren Shekarau

Su ma ’ya’yan APC na bangaren tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da aka fi sani da G-7, sun dage cewa zaben da suka gudanar ne halattacce, ba waninsa ba.

Da yake zantawa da Aminiya bayan kammala taron da Kwamitin Shura ya gudanar a karkashin lemar dattawa, Kakakin Kungiyar, Dokta Sule Ya’u Sule, ya ce ’ya’yan jam’iyyar da suke bangaren Sanata Shekarau dukkansu sun yanki tikitin yin takara da suka saya da kudinsu daga uwar jam’iyya kuma ta tantance su kamar yadda yake a dokar jam’iyyar.

Ya ce matsayin tsohon Gwamna Shekarau na daukaka batun shi ne matsayarsu kuma suna da yakinin uwar jam’iyyar ta kasa za ta yi abin da ya dace wajen duba koke-kokensu.

“Mu masu biyayya ne kuma muna nan daram cikin Jam’iyyar APC, kuma za mu saurara mu ga matakin da shugabannin jam’iyyar za su dauka game da zaben shugabannin da aka gudanar,” inji shi.

Idan za a iya tunawa, Alhaji Ahmadu Haruna Danzago ne ya ci zaben shugabancin jam’iyyar da aka gudanar a Janguza da ’ya’yan Jam’iyyar APC magoya bayan G-7 suka gudanar, yayin da Alhaji Abdullahi Abbas da ke samun goyon bayan Gwamnan Jihar, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya ci zaben da aka gudanar a dakin taro na Sani Abacha.

An gudanar da zabubbuka hudu a Legas

Hakazalila a Jihar Legas an samu zabe kashi hudu da aka gudanar, kowane bangare ya hakikance cewa a kan daidai yake.

Zabubbukan da bangaren tsohon Gwamna Akinwunmi Ambode ya gudanar da ’ya’yan Kungiyar Lagos4Lagos da na Conscience Forum, ya nuna an gudanar da zabubbuka kashi hudu ke nan a jihar inda jam’iyyar ta karbi wanda bangaren Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gudanar.

Kasim Bakare, Kakakin Kungiyar Lagos4Lagos ya ce zaben da suka gudanar shi ne ingantacce kuma shi ne uwar jam’iyya za ta yi amfani da shi.

Da aka tuntubi Sakataren Yada Labarai na bangaren Ambode, kuma tsohon sakataren watsa labaransa, Habib Haruna ya ki cewa komai game da lamarin, inda ya ce ba ya da wata masaniya a kai domin ba ya gari.

Ba a gini da tubalin toka – Okorocha

Shi kuma tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana zabubbukan shugabannin APC da aka gudanar a jihar a matsayin wani abin kunya.

Da yake magana ta hannun Kakakinsa, Sam Onwuemeodo,

ya ce akwai hukuncin kotu da ya tabbatar da Mista Daniel Nwafor a matsayin Shugaban Jam’iyyar a jihar.

Ya ce, “Ba ni da wata masaniya na wani zabe da aka gudanar domin a iya sanina akwai hukuncin kotu da ya tabbatar da Daniel Nwafor a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Imo.

“Hukunci ne da hatta wata jam’iyya ma ta daukaka kara a kai kuma wannan ne matsayata har zuwa wannan lokaci.

“Ka ga ke nan babu yadda za a yi ka dora gini a kan ginin da babu shi tun farko.

“Har yanzu Daniel Nwafor ne Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Imo,” inji shi.

‘A gaggauta rusa Kwamitin Buni’

Wani jigo a Jam’iyyar APC daga shiyyar Kudu maso Yamma, Cif Jackson Lekan Ojo, ya bayyana wa Aminiya ta tarho cewa masu ruwa-da-tsaki a Jam’iyyar APC su yi gaggawar rusa kwamitin da Gwamna Mai Mala Buni yake shugabanta.

Ya ce, “Kwamitin Buni ba ya da wata kwarewa don haka a rusa shi kawai.

“Abin da kawai suka iya shi ne sun dauka suna kama kifi ne amma ba su san suna janyo wa kansu damuwar da za ta kekketa su ba ne.

“Mutanen da suka janyo za su koma jam’iyyun da suka baro.

“Akwai baraka sosai a jihohin Ogun da Legas da Imo da Ebonyi da Akwa Ibom da Kuros Riba da Bauchi da kusan ko ina,” inji shi.

Kwamitin Sansanci ya fara lallabar fusatattu

A jawabin Shugaban Kwamitin Sansanci na Jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya roki duk wadanda aka bata wa rai da su rika girmama hukuncin jam’iyyar.

“Wannan jam’iyyarmu ce kuma dole mu samo mata mafita ta hanyar mutunci; mu ne a kan mulki don haka ya kamata mu yi iya kokarinmu; mazanmu da matanmu, mu zamo masu biyayya ga jam’iyyarmu.

“Akwai umarnin da jam’iyya ta bayar, don haka ya kamata mu yi kokari mu tsaya a nan.

“Idan wani yana da wani korafi a kai sai mu duba mu gani amma abin da ba za mu bukata ba shi ne gudanar da tagwayen zabubbuka saboda ba za su amfanar da jam’iyyar ba, matsayar jam’iyyar game da haka a fili yake,” inji shi.

Sai ya tabbatar da kokarin da kwamitinsa yake yi wajen sasanta wadanda aka fusata a cikin jam’iyyar, inda ya ce sun san da rikicin bukatu na cikin gida a cikin jam’iyyar, amma abin da za su iya yi kawai shi ne sasanci a karkashin dokoki da kuma umarnin da jam’iyya ta bayar.

Kan haka ne Mataimakin Magatakardar Jam’iyyar ta Kasa, Mista Yekini Nabena, ya ce babu batun kai jam’iyyar zuwa kotu bisa dalilin zabubbukan shugabannin jam’iyyar da aka gudanar.

Ya ce, “Babu wasu bangarori a Jam’iyyar APC kuma babu wasu tagwayen zabubbuka da muka sani.

“Mun san jam’iyya ta tura kwamitocin zaben shugabanni zuwa kowace jiha domin gudanar da zabe kuma za su mika rahotonsu don haka a kan wane dalili ne wani zai kai jam’iyya kara a kotu?”.

Abin da ya sa aka samu matsala – Mansur Soro

Wani dan Majalisar Wakilai daga Jihar Bauchi, Alhaji Mansur Manu Soro ya ce duk da cewa ba za a iya kauce wa sabani a zabubbuka a matakin jam’iyya ba, amma ya kamata shugabannin Jam’iyyar APC su yi dubi sosai game da lamarin da sanin abin da ya kamata don magance abubuwan da aka gani a zabubbukan da suka gabata.

Sannan ya ce jam’iyyar ta haifar wa kanta gibi yadda ta bar wani bangare da yake da matukar muhimmanci, wato Kwamitin Amintattu babu kowa a ciki, wanda hakan ya dada taimakawa wajen raunata hanyoyin samar da mafita da sasanci game da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar.

Daga Ismail Mudashir da Balarabe Alkassim da Saawua Terzungwe (Abuja) da Jude Aguguo Owuamanam (Owerri) da Abdullateef Aliyu (Legas) da Ado Abubakar Musa (Jos) da Hameed Oyegbade (Osogbo) da Clement A. Oloyede (Kano).