Kwamitin Majalisar Dokokin kasar Libya ya ce zaben shugaban kasar da aka tsara gudanarwa ranar Juma’a ba zai yi wu ba yadda aka tsara.
Majalisar ta sanar da haka ne a yaran Laraba, duk da cewa ana ganin zaben na da matukar muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
- An damke masu yi wa ’yan bindiga safarar karuwai
- Rayukan ’yan Najeriya ba su dami Buhari da gwamnonin Arewa ba —ACF
Shugaban kwamitin, Al Hadi al-Sagheer, ya aike wa Shugaban Majalisar, Aguila Saleh, cewa zaben ba zai gudana kamar yadda aka tsara ba kuma ba tare da sanya wata ranar zaben ba.
Ya ce bayan duba da yanayin tsaron kasar da kuma rohoton kotu kan zaben da kuma gama shirya kayan aikin zaben, zaben ba zai yi wu ba kamar yadda aka tsara da farko ba.
Bugu da kari, har yanzu hukumar zaben ba ta fitar da tabbataccen sunayen ’yan takarar shugaban kasar ba, a sakamakon kalubalen da ake fuskanta dangane da dokokin zaben.
Har ila yau, Al-Sagheer ya bukaci Saleh da ya dawo ya karbi ragamar majalisar bayan ya ajiye mukaminsa domin tsayawa takarar shugabancin kasar.
Har zuwa yanzu dai wadanda ake sa ran za su tsaya takara a zaben sun hadar da Saif al-Islam, dan tsohon shugaban kasar, Muammar Gaddafi da kuma Janar Khalifa Haftar wanda ke da iko da Gabashin kasar mai arzikin mai.
Kasar Libya dai na fama da matsalar tsaro da tashin hankali tun bayan hambarar da gwamnatin Gaddafi a 2011.
A karshe ana ganin wannnan zabe da za a gudanar wani yunkuri na Majlisar Dinkin Duniya ne ne ganin an kawo karshen tashin hankali da ake fuskanta a kasar.