Masu fada a ji a jam’iyyar PDP sun umarci daliget da su kada kuri’a daidai da jerin sunayen ‘Unity List’ a babban taron jam’iyyar na kasa da ke gudana.
Majiyoyinmu a hedikwatar PDP sun shaida mana cewa jerin sunayen an fitar da shi ne tun kafin zuwan babban taron jam’iyyar da ake gudanar da zaben.
- ‘Arewa Maso Gabas ya kamata PDP ta ba takara a 2023’
- 2023: Ba za mu bari a kai takara Kudu saboda son kai ba – Sule Lamido
Wakilinmu bai samu ganin kwafin jerin sunayen ba, amma majiyarmu ta ce, “A babban taron jam’iyyar na baya an yi amfani da ‘Unity List’ a wannan ma za a yi amfani da shi.”
‘Unity List’ din dai na dauke da sunaye da mukaman wadanda idan suka ci zaben za su zama mambobin Kwamitin Gudanarwar na Kasa (NWC) a jam’iyyar.
Duk da cewa an cimma daidaito a kan yawancin mukaman da ke kwamitin gudanarwar na kasa, hakan bai samu ba a kan wasu, wanda ya sa aka fitar da jerin sunayen domin saita wa daliget alkiblar yadda za su yi zaben.
Idan ba a manta ba a 2017 PDP ta yi amfani da ‘Unity List’ wanda ya kai ga samar da Kwamitin Gudanarwa na Kasa karkashin jagorancin Prince Uche Secondus.