Reshen masu aikawa da rahotanni na Kungiyar ’Jarida ta Najeriya a Jihar Osun ta yi Allah Wadai da harin cin zarafi da aka kai wa wakilin kafar yada labarai ta Daily Trust a jihar.
An kai wa wakilin Daily Trust da kuma gidan talbijin na Trust TV Hameed Oyegbade hari ne a yayin da yake gudanar da aikinsa a ranar Asabar 15 ga watan Oktoba lokacin da ake zaben kananan hukumomin jihar
- INEC ta ba Adeleke takardar shaidar lashe zaben Gwamnan Osun
- Zaben Osun: Masu zanga-zanga sun taru a matattara sakamako
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar wacce sakatarenta, Lateef Saki, ya sa hannu ta ce, harin da kuma cin zarafin dan jaridar sun faru ne a wurin tattara kuri’u a harabar Sakatariyar Karamar Hukumar Osogbo ta Kudu.
Wasu ’yan Jam’iyyar APC ne suka far wa Hameed Oyegbade, suka barazanar kashe shi da tare da kokarin farfasa masa kayan aiki sannan suka yi masa korar kare daga wurin.
’Yan jam’iyyar sun hana ’yan jarida shiga harabar don gudanar da aikinsu, ana haka sai wasu da ake suka far wa Oyegbade, wanda ya yi satar shiga wurin tare da kokokarin gudanar da aikinsa na jarida.
Dan jaridar ya koka da rashin tabuka komai da wasu ’yan sandan da ke wurin suka yi, daga karshe har cewa suka yi lallai ya bar wurin.
Kungiyar ’yan jaridun ta ce ba za ta lamunta ba.