✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Ondo: Jam’iyyu sun sauya ‘yan takara

Su jam'iyyar PDP sun sauya 'yan takarar Gwamna da Mataimakin Gwamna

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce jam’iyyu hudu daga cikin masu karawa a zaben Gwamnan Jihar Ondo na ranar 10 ga watan Oktoba sun sauya ‘yan takararsu.

Shugaban Kwamitin Wayar da Kai na INEC Festus Okoye, bayan taron hukumar kan zaben Ondo da na bayansa, ya ce hukumar ta kuma fitar jerin sunayen ‘yan takarar zaben a karon karshe.

“Jam’iyyar ZLP ta sauya dan takarar gwamnanta yayin da ADC, ADP da PDP kuma suka sauya ‘yan takarar Mataimakin Gwamnansu.

“Bisa tanadin dokar zabe, damar jam’iyyu na sauya ‘yan takararsu ta kare daga karfe 6.00 na yamma, ranar 18 ga Agusta, 2020”, inji shi.

Ya bukaci jama’a da su duba shafin hukumar domin ganin jerin sunayen ‘yan takarar, tare da kiran jam’iyyu da su kiyaye dokokin zabe.

“Hukumar ta wallafa jerin sunayen a ofishinta na Jiha da Kananan Hukumomin Jihar Ondo da kuma shafinta INEC na intanet”, inji Okoye.

Sanarwar da INEC ta fitar a baya ya nuna da jerin sunayen ‘yan takarar jam’iyyu 17 a zaben na Ondo.

Masu ke hankoron darewa kujerar gwamnan sun hada da babbar jam’iyyar adawa ta PDP wanda Eyitayo ke yi wa takara da kuam Gwamna Rotimi Akeredolu na APC da ke neman tazarce.