’Yan takarar Jam’iyyar NNPP a zaben cike gurbin da aka gudanar a Kano sun yi nasara a mazabu biyu daga cikin ukun.
Muhammad Bello Butu-Butu ya lashe zaɓen gidan majalisa mai wakiktar Rimin Gado/Tofa a yayin da da Alhassan Zakariya Ishaq ya lashe ne Kura/Garun Malam.
Jami’in zabe na zaben Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya bayyana cewa Bello Muhammad Butu-Butu na NNPP ya samu kuri’u 31,135 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar APC da ya samu kuri’u 25,577.
Kotun daukaka kara ce ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 33 da ke mazabar Rimin Gado/Tofa.
Hakazalika, jami’in zabe na Kura/Garun Malam, Farfesa Shehu Musa Galadanchi ya bayyana cewa Dr. Ishaq na NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke babban abokin adawansa, Musa Hayatu Daurawa na APC wanda ya samu kuri’u 30,803.
Idan ba a manta ba kotun daukaka kara ta umarci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 20 dake mazabar Kura/Garun Malam.
Aminiya ta ruwaito cewa INEC ta soke zaben Kunchi/Tsanyawa sakamakon saba dokar zabe da ’yan daba da suka yi a yayin zaben.
Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wasu ’yan bangar siyasa l dauke da makamai a wuraren da aka gudanar da zaben a Tsanyawa.