A yammacin ranar Alhamis ne dai dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan da aka gudanar a jahar Kanon Najeriya Abba Kabir Yusuf, ya shigar da kara a gaban kotun kararrakin zabe da ke zaman ta a titin Miller a cikin babban birnin jahar.
Abba Kabir Yusuf, ya shaida wa BBC cewa, sun je kotun ne domin su gabatar da dukkan takardunsu na korafe-korafe da lauyoyinsu suka tsara a kan zabukan da suka gudana na gwamna.
Dan takarar gwamnan ya ce, a zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, hukumar zabe ta kasa a jihar ta sanar da sakamakon inda ta bayyana cewa jam’iyyar PDP ce ke kan gaba.
To amma daga bisani hukumar ta ce zaben bai kammala ba, inda aka sake yin wani a ranar 23 ga watan na Maris aka kuma bayyana dan takarar jam’iyyar APC, wato gwamna Ganduje a matsayin wanda ya samu nasara, bayan kuma kowa ya san duk abubuwan da suka faru a yayin zaben, in ji Abban.
Abba Kabir Yusuf, ya ce su a wajensu sam ba su yarda da sakamakon zaben da aka yi na biyu ba.
Ya ce, sun dauki matakin kin amincewa da sakamakon zaben ne saboda zabe ne wanda kowa a Najeriya ba ma a Kano kadai ba har da ma wasu kasashen duniya suka yi alla-wadai da shi.
Dan takarar gwamnan a jam’iyyar ta PDP a Kano, ya ce: “An yi zabe ne na son-kai, an hada baki da jami’an tsaro, kana an hada baki da su kansu jami’an hukumar zabe, an sassari wasu, an ji musu ciwo, sannan an ci mutuncin mutane.’
Ya ce baya ga wadannan abubuwa da aka yi, hatta wakilan jam’iyyu an kore su daga rumfunan zabe.
Abba Kabir Yusuf, ya ce cin mutuncin ma har ‘yan jarida ya shafa.