✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben kananan hukumomin Kano bai yi ingancin na baya ba

A ranar Lahadin wannan makon ce Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, Dokta Sani Lawal Malumfashi ya bayyana wa manema labarai cikakken…

A ranar Lahadin wannan makon ce Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, Dokta Sani Lawal Malumfashi ya bayyana wa manema labarai cikakken bayanin sakamakon zaben da Hukumarsa ta gudanar a dukkan Majalisun kananan Hukumomin jihar 44, a ranar Asabar 17 ga wannan watan na Mayu. Kamar yadda ya fadi, wanda kuma ya ce shi ne abin da Turawan zaben da suka kula da kananan hukumomin suka bayyana a kananan hukumominsu jim kadan bayan kammala zaben, dukkan `yan takarar  Jam`iyyar APC, na neman shugabancin Majalisun kananan Hukumomin 44, da na Kansilolinsu 484, su suka lashe zaben, ma`ana ba kujera daya da ta subucewa jam`iyya mai mulki.
 Dokta Sani Malumfashi ya bayyana yadda aka gudanar da zabubbukan da cewa an yi su cikin gagarumar nasara, nasarar da ya ce ta samu ne daga irin yadda dukkan mutanen jihar suka bada hadin kai, da haka yake ganin nasarar ta dukkan mutanen jihar ce. Amma kuma bai waiwayi irin koke-koken da `yan adawa suka yi ba, na kura-kurai da magudin da suke zargin an tafka, musamman rashin gudanar da zabe a wasu wurare da irin aringizon kuri`u da ba a taba samun su ba a tarihin zabe a jihar, alhali tun farko ya bada tabbaci ga jama`ar jihar za su gudanar da kome cikin gaskiya da adalci.
 Alal misali Hukumar zaben ta jihar Kano, ta yiwa jama`ar jihar alkawarin isar kayayyakin aikin zabe a dukkan tashoshin zabe 484, akan lokaci ta yadda za a fara tantance masu kada kuri`a daga karfe 8 na safe zuwa 10 da rabi na safen, kuma daga wannan lokaci za a fara kada kuri`a har zuwa karfe 3 da rabi na rana, lokacin da za a rufe tashoshin zabe a fara kirga kuri`a. Amma kamar yadda rahotannin kafofin yada labarai masu zaman kansu suka tabbatar, kusan a `yan mazabu kalilan aka samu tabbatuwar hakan. Rahotannin da wadancan kafofin yada labarai suka rika kawowa a daidai lokacin sun tabbatar da cewa akasarin kayayyakin aiki ba su isa tashoshin zaben ba sai bayan karfe 9 da rabi na safe a wasu ma har zuwa wucewar sha biyun rana, kana ma`aikatan zaben suka bayyana da kayayyakin aikin.
Bayan waccan gagarumar makara da ta zama kusan rowan dare a cikin zaben, kafofin yada labaran sun ruwaito cewa, a wasu tashoshin ma bayan makarar kayayyakin aikin da aka samu in ji wadancan kafofin yada labarai da ba na gwamnati ba, hatta fom-fom ba da za a ciki sakamakon zabe, baa je das u wasu tashoshin ba. Haka dai labarin kura-kurai sukai ta kasancewa a cikin yinin zaben. Ya yin da a gefe daya kafofin yada labarai mallakar gwamnatin jihar sukai ta bayyana cewa kome na tafiya daidai, ba inda aka samu wata matsala ko kadan.
Hatta shi kansa gwamnan Jihar Injiniya Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso a lokacin da yake kada kuri`arsa a mazabar Kwankwaso Malamai, ri ga Malam masallaci ya yi inda ya fadawa manema labarai cewa kome na gudana lami lafiya kamar yadda aka tsara, yana mai cewa “kura-kuran da ake fadin an samu a cikin zaben kamar na isar kayayyakin zabe a makare, ba su isa su bata sahihancin zaben ba. Shi ma Shugaban Hukumar zaben Dokta Sani Lawal Malumfashi irin wannan shaida ya bayar akan sahihancin zaben a daidai tsakiyar ana gudanar da shi.
Sakamakon zaben da shugaban hukumar ya bayar ga manema labarai a ranar lahadi ya tabbatar da cewa Jam`iyyar APC, mai mulkin jihar ita ta lashe dukkan kujerun shugabannin majalisun kananan Hukumomi 44, dana Kansiloli 484, na jihar. Alhali tarihin sakamakon zaben kananan hukumomi a jihar, bai taba tabbatar da haka ba. Alal misali a zaben da gwamnatin jam`iyyar APP ta gudanar a shekarar 2004, jam`iyyar adawa ta PDP ta samu nasarar kujeru 3, na majalisun kananan hukumomi da kansiloli 40. A na shekarar 2007, da gwamanatin ANPP din ta sake gudanarwa jam`iyyar adawa ta PDP, ta sake samun nasararlashe kujerun majalisun kananan hukumi 3, da kansiloli 20, amma a wannan karon jam`iyyar PDP da take jam`iyyar adawa ko kansila daya bata samu ba.
Da bayyana wannan sakamakon zabe an ruwaito  Gwamna Kwankwaso yana fada wa manema labarai cewa sun yi tuwassali da irin ayyukan alherin da suka yi wa jama`ar jihar, ayyukan da ya ce ana ina ganinsu a ko ina a fadin jihar, wadanda suka sa jama`ar jihar suka zabe su. Alhali a gefe daya `yan adawa na zargin cewa ko kusa ba a yi zabe ba a kusan dukkan fadin jihar.inda aka kwatanta ma rashin isar kayayyakin aiki da wuri da wai hana `yan adawa su kada kuri`unsu, su kadai sun isa a san cewa ba a yi sahihin zabe ba, bare a ce jam`iyyu adawa da suka shiga zaben sun fadi. A shirin Inda Ranka na gidan Radiyon Freedom, inda gwamna Kwankwaso ya sake nanata wancan tuwassali, ya kuma ruwaito wani dan adawa mai suna Alhassan Nakande daga karamar hukumar Shanono yana cewa a cikin Cibiyar addinin Islama ta garin na Shanono aka shiga da dukkan kayyakin zaben karamar hukumar aka raba kuri`u ga `yan takarar na APC, sannan aka bayyana sakamakon, alhali wannan Cibiya, wai ba mazaba bace bare kuma Cibiyar tattara bayanan zaben. Rashin gudanar da zabe da ake zargin ba a yi ba a Shanono shi ake zargin an yi a kananan hukumomin Rogo da Birni da kewaye da wasu wurare, in ji `yan adawar.
 Masu kula da al`amurran siyasa a jihar sun fara fassara wannan sakamakon zabe da APC ta ce ta samu, a zaman riga Malam masallaci a zabubbukan kasa masu zuwa a badi, ta yadda muddin sakamako suka sha bamban daga irin wanda ta samu yanzu, za ta iya kururuwar cewa an yi mata magudi, alhali kamar yadda tarihin siyasar jihar ya tabbatar zuwa yanzu, ba wata jam`iyya da ta taba tsarin cinye dut.
Babbar nasarar wannan zabe a wannan karon, bai wuce irin yadda aka yi shi ba tare da wani mummunan tashin hankali ba, duk da yake rahotanni sun tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu a lokacin zabe. daya a garin Yaryasa da ke cikin karamar hukumar Tudun Wada, inda rikici ya barke tsakanin `yan APC da PDP, yayin da a Kwanar dangora da ke cikin karamar hukumar kiru a cikin harbin da `yan sandar kwantar da tarzoma suka yi wa wasu matasa da suke biye da matarsu da take dauke da kayayykin zabe, nan ma harbin nasu ya kashe  wata mata ma`aikaciyar asibiti mai suna Talatu, ba ya ga mutane shidda da suka samu raunuka. Zuwa yanzu dai babu wata tartibiyar matsaya da babbar jam`iyyar adawa ta PDP ta ce za ta dauka akan zaben. Allah dai ya kiyaye, amma babu yadda za a yi a murde zabe a ce kuma shugaba ya zauna lafiya.