Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi ya kankama a Jihar Ondo, bayan tantance masu jefa kuri’a a safiyar Asabar 22 ga Agusta, 2020.
Wasu rahotanni sun nuna cewa zuwa karfe 10 na safiya aka fara tantance masu zabe a wasu rumfuna duk da cewa a wasu wuraren an samu jinkiri fiye da haka.
Bullar annobar COVID-19 ta sa aka dage zaben da aka shirya gudanarwa a watan Afrilu, kafin a watan Yuli Shugaban Hukumar Zaben Jihar Ondo, Yomi Dinakin ya sanar cewa za ayi shi a ranar 22 ga Agusta.
A wasu rumfuna da majiyarmu ta ziyarta an samu jinkirin isar kayan zabe.
Wani da takarar Kansilan Jam’iyyar APGA a gundumar Ayeotoro, a Karamar Hukumar Ilaje Agere Olowoloba ya ce zuwa lokacin ba dukkannin rumfunan zaben yankin ne suka samu kayan zabensu ba.
“Rumfar zabe shida ce a Mazabar Ayetoto amma biyar daga cikinsu ne aka kai kayan zabe”, inji shi a lokacin.
A watan Oktoba ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar wanda jam’iyyu 17 za su fafata, ciki har da gwamna mai ci Rotimi Akeredolu.