✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kaduna: Sojoji sun bindige yarinya mai shekara 9 a Makarfi

Ta rasu ne lokacin da sojoji suka zo korar matasan da ke yiwa wani dan siyasa ihu.

Sojoji sun bindige wata yarinya har lahira mai shekara tara a gundumar Gwanki da ke Karamar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna a wata rumfar zabe.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kada kuri’a a zaben Kananan Hukumomi na Jihar na ranar Asabar.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa, Alhaji Yahaya Gwanki ya shaida wa Aminiya cewar yarinyar mai suna Zainab Bala ta rasa ranta ne lokacin da sojoji suka zo korar matasa da ke yiwa tsohon Shugaban Karamar Hukumar ta Makarfi ihun ‘Ba ma so’.

Ya kara da cewa tsohon Shugaban Karamar Hukumar ya zo wata mazaba a Fadamar Gwanki a sanadiyar tsayawar da naurar zaben ta yi.

Yahaya Gwanki ya kara da cewa matasan da ke wurin saboda ganin yadda dan takarar yake magana da malaman zabe sai suka kama ihu ‘Ba ma so, ba ma so’.

Hakan, a cewarsa ne ya sa shi kuma ya kira sojoji don su kori masu yi ihun, daga nan ne harsashi ya sami ita yarinyar, ya kuma yi sanadiyyar mutuwarta nan take.

Da muka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce za su kamo shi dan takaran saboda doka ba ta bayar da dama ga sojoji su je rumfunan zabe ba.

“Zamu yi muku cikakken bayani da zarar mun kamo shi,” inji Jalige.