✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamnoni: A guji siyasar ko a mutu, ko a yi rai —Jonathan

Tsohon shugaban kasar, ya shawarci jama'a da su zabe lafiya.

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya shawarci ’yan siyasa da su guji siyasar ko a mutu, ko a yi rai, domin masu muradin yin mulki ba sa tilasta jama’a.

Jonathan ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis a Jihar Bayelsa jim kadan bayan ya kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Douye Diri da ya rasa mahaifinsa, Pa Abraham Diri.

Aminiya ta ruwaito cewa Bayelsa mahaifar tsohon shugaban kasa za ta gudanar da zaben majalisar dokokin jihar ne kawai a ranar Asabar, yayin da zaben gwamna zai gudana a ranar 11 ga Nuwamba, 2023.

Mai magana da yawun Gwamna Douye Diri, Mista Daniel Alabrah, ya shaida wa manema labarai a wata sanarwa a ranar Alhamis cewa, Jonathan ya kuma jaddada cewa kamata ya yi siyasa ta zama hanyar yi wa jama’a hidima, ba ta son kai ba.

Ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su jira lokacin da Allah Zai ba su damar da za su yi shugabanci ba ta karfin tsiya ba.

Jonathan ya bayyana cewa, a tsarin dimokuradiyya, jama’a suna taka rawar gani, inda ya yi mamakin dalilin da ya sa masu burin shugabanci ke son tilasta wa jama’a su zabe su.

Ya kuma shawarci al’ummar jihar da su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali a lokacin zaben.

“Shugabanci ba da karfi ake yin sa ba. Abu ne hidima. Don haka, idan kuna son jagorantar jama’a, ba za ku iya kashe su ba da nufin jagorantarsu ba.

“A Bayelsa, kalubalen da za a fuskanta ba mai yawa ba ne saboda ba za mu yi zaben gwamna a ranar Asabar ba. Amma ina kira ga mutanenmu da su rika tafiyar da rayuwarsu yadda ya kamata,” in ji Jonathan.

Jonathan dai ya sha kaye a hannun shugaba Buhari a zaben 2015, kuma ya amince da kayin da ya sha, inda ya taya Buhari murnar lashe zaben.