✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Gwamna: Ya kamata ’yan siysar Jihar Bauchi su natsu

’Yan siyasa da al’ummar Jihar Bauchi ya wajaba mu yi karatun ta-natsu kan zaben Gwamnan Jihar mu mai zuwa. Kukan da ’yan siyasa da al’ummar…

’Yan siyasa da al’ummar Jihar Bauchi ya wajaba mu yi karatun ta-natsu kan zaben Gwamnan Jihar mu mai zuwa.

Kukan da ’yan siyasa da al’ummar jihar ke yi kan gazawar gwamnatin jihar a shekara uku, zai zamo kukan banza idan ’yan takarar Gwamnan Jihar suka gaza hadewa wuri guda don tunkarar zaben mai zuwa.

Lokaci ya yi da manyan ’yan takarar da suka fito daga jam’iyyun PDP da PRP da ANPP da sauransu za su hade su dauki mikati domin kawo canji mai ma’ana a jihar nan. Amma babu yadda za a yi ku shiga wannan zabe a rarrabe sannan ku sa ran za ku samu nasara. Duk yadda mu al’ummar Jihar Bauchi muka kai da daura harama don kawo canji mai ma’ana a jiharmu ba za mu yi nasara ba, sai mun dunkule wuri daya. Domin masu iya magana sun ce kisan baki sai taro, don haka wajibi ne ’yan siyasar Jihar Bauchi su zauna su cire son zuciya su fitar da dan takara guda daya mai mutunci da natsuwa da sanin ya kamata da gaskiya da amana a hadu a ba shi goyon baya.

Wajibi ne mu kawo karshen yaudarar da wannan gwamnati take yi ga ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati da ’yan fenso da `yan acaba da Keke NAPEP da zaluntar wadanda bala’in iska da ruwa suka shafa a wannan jiha a kusan shekara guda da ta gabata.

Don haka ku sama wa kanku mafita domin lokaci ya yi da za ku canja. Allah Ya nufe ku da samun fahimtar hakan domin cire al’ummar Jihar Bauchi daga kunci da dimuwar da suke ciki .

Alhaji Gambo Bababa, Shugaban Kungiyar Masu Sarrafa Magungunan Gargajiya ta Jihar Bauchi, 08023622651, 07032096837