A gobe Asabar ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar da zabe Gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa, inda ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin wannan aiki.
Sai dai kuma a yayin da jam’iyyun da za su fafata a zaben suka kammala kamfe a jiya Alhamis, ana ci gaba da zaman dar-dar sakamkon yadda ake samun musayar munanan kalamai a tsakanin manyan jam’iyyun kasar nan biyu APC da PDP.
Baya ga musayar zafafan kalamai tsakanin ’yan siyasar, an kuma rika samun rikice-rikice a tsakanin magoya bayansu, inda a ranar Talatar da ta gabata, sai da aka samu daruruwan ’yan daba da suka jawo hargitsi a yayin wani taron masu ruwa-da- tsaki a zaben na gobe suka hallara a Lakwaja, fadar Jihar Kogi, don rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin zaben.
Sananna a Bayelsa an kai hari da bindigogi a kan wani gangamin Jam’iyar PDP a shekaranjiya Laraba inda aka samu rahoton rasuwar mutum daya.
Taron sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na Lakwaja wanda sai da ’yan sanda suka jefa borkono mai sa hawaye kafin tarwatsa ’yan bangar siyasar, ya samu halartar Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu da Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu da Daraktan Hukumar Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Sha’ibu Ibrahim da wadansu manyan masu ruwa-da-tsaki a sha’anin zabe.
Hatsaniyar ta barke ne a lokacin da ’yan daba suka kai hari kan ’yar takarar Gwamna ta Jam’iyyar SDP,, Misis Natasha Akpoti da kuma Shugaban Jam’iyyar ta Jihar Kogi, Mouktar Atima.
Aminiya ta kalato yadda jami’an soja da hadin gwiwar ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suka ceto ’yar takarar da shugaban jam’iyyar, yayin hatsaniyar.
A kokarinsu na ganin an yi zaben lafiya, kungiyoyin kabilar Igala mazauna kasashen waje na Ukomu Igala Organisation da kuma Igala Organisation Foundation, sun gargadi matasa su guje wa duk wani abu da ka iya kawo tashin hankali a lokacin zaben na gobe.
Shugaban Kungiyar UIO, Dokta John Onuh da Sakatarensa, Mista Amos Amodu sun fitar da wata sanarwa, inda suka ja hankalin kasashen duniya da sauran masu kaunar zaman lafiya game kan tabarbarewar tsaro a Jihar Kogi, gabanin zaben na gobe.
Yayin da ita kuma Kungiyar IHF, ta bakin shugabanta, a wani taron manema labarai a Abuja, ta ce rahotannin farko da ta samu, sun nuna yadda shirye-shirye gabanin zaben suke kara haddasa fargaba a tsakanin al’ummar Jihar Kogi da duk wani dan Najeriya mai kishin kasa.
’Yan takara 24 za su fafata a zaben Kogi
A zaben na gobe Asabar, ’yan takara 23 ne Hukumar INEC ta tantance domin fafatawa a zaben Gwamnan Jihar Kogi da farko; sai dai kuma hukumar ta kara sanya sunan Barista Natasha Akpoti, ta Jama’iyyar SDP wacce a da hukumar ta ce ba ta cancanta ba. Wannan ya biyo bayan umurnin da kotu ta bayar ne cewa hukumar ta sanya sunanta cikin ’yan takarar. Don haka ’yan takara 24 ne za su fafata a zaben kujerar Gwamnan Jihar Kogi.
Zaben dai ana ganin zai yi zafi, musamman a tsakanin Gwamna mai ci, Yahaya Bello wanda yake neman dawowa kujerar a karo na biyu da kuma Injiniya Musa Wada na Jam’iyyar PDP.
Dukkan ’yan takarar suna kokarin ganin sun samu amincewar jama’a don sun lashe kujerar. Kuma masu ruwa-da-tsaki a jam’iyyun sun yi ta shigi-da-fici, musamman wajen “kai dauki da dauni” ga al’ummomin da suke neman goyon bayansu.
Wadansunsu sun bayar da kyautar motoci da babura da abinci da sutura da sauran kayan alatu ga magoya bayansu don haka ne ake samun wandaka a fadin jihar kafin zaben.
Sai dai kuma ana ganin dan takarar da zai yi wata bajinta bayan biyun na farko ita ce Natasha duk da yake ta samu an sanya sunanta ne mako daya kacal kafin zuwan zaben.
Yahaya Bello, dan takarar APC
Yahaya Bello ne Gwamna mai ci, wanda kuma Jam’iyyar APC mai mulki ta sake tsayar da shi takara. Bello ya fito ne daga Karamar Hukumar Okene a Kogi ta Tsakiya sannan ya dauki Mataimakinsa Edward Onoja daga Karamar Hukumar Olamaboro ta Kogi ta Gabas. A yayin da ya kaddamar da kamfe dinsa, taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Adams Oshiomhole da gwamnonin jihohin Ekiti da Neja da Kwara da Nasarawa da Yobe da sauransu.
Ana hasashen Bello yana iya lashe zaben, ganin cewa yana da goyon bayan maigidansa a siyasa, wato Bola Ahmed Tinubu jagoran Jam’iyyar APC ta Kasa. Kuma yana da gata wajen Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Adams Oshiomhole da kuma sauran jiga-jigan APC na kasa.
Musa Wada, dan takarar PDP
Injiniya Musa Wada wanda, PDP ta tsayar takarar Gwamnan Jihar Kogi ya fito ne daga Karamar Hukumar Dekina, dan uwan ga tsohon Gwannan Jihar, Idris Wada ne kuma surukin tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Idris.
Wada ya samu tarbar dimbin magoya bayansa a yayin kaddamar da kamfe dinsa a filin wasa na garin Lakwaja. Kuma taron ya samu halartar Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa, Uche Secondus da gwamnonin jihohin Bayelsa, Sariake Dickson da Oyo, Seyi Makinde da Bala Mohammed na Bauchi da Aminu Tambuwal na Sakkwato da na Taraba da wasu jigogin Jam’iyyar PDP.
Wada yana kyautata samun nasara ganin irin goyon bayan da yake samu daga Kogi ta Gabas, inda ya fito. Musamman ganin yadda babbar kungiyar ci gaban al’ummar Igala ta ba da umarni ga dukkan ’ya’yanta cewa su mara masa baya a ranar zabe.
Natasha Akpoti, ’yar takarar SDP
Barista Natasha ita ce ’yar takarar da Jam’iyyar SDP ta tsayar a zaben Gwamnan Jihar Kogi na gobe. Ganin cewa kotun ta ba da umarni ga Hukumar INEC ta sanya sunanta a cikin ’yan takarar da za su fafata, ana ganin cewa ita ce za ta taka rawa sosai a wannan zabe. Ta fito ne daga Karamar Hukumar Okehi da ke Kogi ta Tsakiya, wato inda Gwamna Bello ya fito.
Duk da yake mako daya kafin zaben ta samu aka saka sunanta, masu bin kadin zabe na ganin Natasha tana da tagomashi a wurin magoya bayanta. Ba ma kamar yadda suka ga ta jajirce har ta samu nasara a kotu, inda kotun ta ba da umarnin a sanya sunanta; bayan Hukumar INEC ta ce ba ta cancanta ba.
Hukumar INEC da ’yan sanda sun shirya tsaf
Hukumar INEC ta fitar da sanarwar cewa ta shirya tsaf don gudanar da tsabtataccen zabe a Jihar Kogi. Ta sanar da haka ne ta bakin shugabanta a Jihar Kogi, Farfesa James Apam. Ya ce sun karbi mafi yawan kayan aiki da suke bukata don gudanar da zaben, sannan sun dauki ma’aikata na wucin-gadi da za su yi aiki da su wajen zaben.
Shi ma da yake bayani dangane da irin shirin da suka yi, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kogi, Hakeem Busari cewa ya yi za su sanya duk irin matakan tsaron da suka kamata, don haka masu zabe su kwantar da hankalinsu, su fita su kada kuri’unsu a gobe.
A Bayelsa APC ta zargi PDP da buga kuri’un jabu
A Jihar Bayelsa, Jam’iyyar APC da ke kan gaba wajen hamayya, ta zargi Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar da buga kuri’un bogi da kuma sauran muhimman kayayyakin zaben a cikin gidan Gwamnatin Jihar ta Bayelsa da zimmar yin kwange a zaben na gobe.
Jam’iyyar APC ta ce wani binciken farko da ta yi ya gwada yadda ake buga takardun bogi na zaben a wani boyayyen wuri cikin Gidan Gwamnatin Jihar a birnin Yenagoa.
Wani dan Kwamitin Tsaron Yakin Neman Zaben Jam’iyyar, Ebimobowei Tamarapriye, cikin wata sanarwa a Yenagoa, ya yi kira ga Hukumar INEC da ’yan sanda da sauran jami’an tsaron Najeriya su gaggauta gudanar da bincike game da zargin.
Haka kuma, a Jihar Bayelsa, an samu rahoton hatsaniya nan da can, gabanin zaben na gobe. A Larabar da ta gabata, ’yan bindiga sun hallaka wasu mutum biyu a Karamar Hukumar Nembe, lokacin da ’yan bangar siyasa dauke da makamai suka yi dirar mikiya a wajen taron yakin neman zaben Jam’iyyar PDP a jihar.
Wani direban tashar rediyon jihar na daga cikin wadanda suka rasa ransu. Janar Manajan gidan radiyon ya tabbatar da kisan direban. Haka kuma akwai wani da ya rasa ransa dan jam’iyyar PDP.
Aminiya ta fahimci cewa dan Jam’iyyar PDP da aka hallaka, an harbe shi ne yayin da suke tafiya cikin wata motar da ke dauke da ’yan jam’iyyar zuwa wajen wannan gangami. Wadansu mutum hudu a motar sun yi rauni.
Yadda abin ya faru, kamar yadda Aminiya ta kalato, wadansu ’yan bindiga ne suka tarwatsa gangamin a Karamar Hukumar Nembe, ta hanyar harbe-harbe a wajen taron, lamarin da ya sanya kowa ya ranta a na kare.
Basaraken Ebira ya yi kira ga ’yan siyasa
Game da zaben na gobe a Jihar Kogi, Sarkin Kasar Ebira, Ohinoyi na Ebira, Alhaji Ado Ibrahim ya sake kira ga ’yan siyasa da su guje wa siyasar-ko-a-mutu-ko-a-yi-rai. Ya shawarce su cewa maimakon bakar gaba a tsakaninsu, kamata ya yi su mayar da hankali wajen ci gaban jihar.
Sarkin ya yi kiran ne a garin Okene, yayin wata ziyara da Kungiyar CPI, mai kula da rainon yara ta kai masa, a matsayin tarurrukan wayar da kan jama’a a mazabun Kogi ta Gabas da ta Tsakiya.
Sarki Ibrahim ya ce, bai kamata a dauki siyasa a zaman abin da zai farraka al’ummomin jihar ba, inda ya ce ’yan siyasa a Najeriya ba su da sanin ya kamata, wanda shi ne ginshikin ci gaban kasa.
Ya ce Jihar Kogi za ta ci gaba da zama dunkulalliya. “Kasa za ta ruguje, a duk lokacin da al’ummarta suka kasance babu aminci a tsakaninsu kuma ba su yarda da juna ba. Idan da a ce dama can ’yan siyasa sun san ya kamata daga farko, to kuwa da babu bukatar sai an yi ta gangamin kada a tayar da zaune-tsaye a lokacin zabe,” inji Sarkin.