Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ba da umarnin hana zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 11:59 na safiyar Juma’a zuwa 6.00 na safiyar Asabar, a Jihar Edo, inda za a yi zaben gwamna a ranar Asabar.
Mohammed Adamu ya ce rundunarsa ba za ta lamunci tashin hankali ko satar akwati ko kasuwancin kuri’u ko kalaman nuna tsana ko duk wani abin da zai yi tasgaro ga zaben ba.
- Fani-Kayode na neman marubuciya ta ba shi diyyar biliyan biyu
- Jami’an lafiya 41,000 sun harbu da COVID-19 a Afirka —WHO
Za a bude makarantu ranar Litinin a Taraba
Sanarwar da Kakakin Rundunar, DCP Frank Mba ya fitar ta ce ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun yi cikakken shiri domin tabbatar da ganin zaben ya gudana cikin lumana da tsafta.
Ya bukaci jama’ar Jihar Edo da su ci gaba da duganar da harkokinsu cikin bin doka ba tare da fargaba ba, sannan su yi tururuwa wajen jada kuri’a.