✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben bana: Jega ya soki malaman jami’a kan bata tsarin zabe

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya zargi malaman jami’o’i da suka yi aikin zabe da hada baki da ’yan siyasa…

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya zargi malaman jami’o’i da suka yi aikin zabe da hada baki da ’yan siyasa a kan rashin ingancin zaben da ya gabata.

Da yake bayani a wajen wani taron kara wa juna sani da aka gudanar a Cibiyar Harkokin Kasuwanci ta Dangote da ke Jam’iar Bayero a Kano, Farfesa Attahiru Jega ya koka kan halayyar da wadansu malaman jami’a suka nuna a lokacin zaben da ya gabata, inda ya ce hakika malaman sun yaudari hukumar zabe saboda irin amincewar da hukumar ta yi da su.

Ya ce,  “Lura da abubuwa marasa dadi da suka faru a yayin zaben bana hatta a kusa da Jami’yar Bayero an samu irin wadannan bayanan aikata ba daidai ba inda ’yan siyasa suka hada kai da malamai wajen bata harkar zabe, wannan na iya taimakawa wajen samar da gurbatattun shugabanni a cikin al’umma.’’

Farfesa Jega ya ci gaba da cewa, “Watakila wadansu su yi zaton ko wa’azi nake yi, amma maganar gaskiya ba mu dauki  bayar  da horon ilimi da kwarewa da bincike da samar da nagartattun mutane da muhimancin da ya dace ba.”

Ya ce, “A tunanina abin da ya jawo matsalar rashin zabe mai inganci a Najeriya shi ne hada kai da ake yi da wadansu masu ruwa-da-tsaki a harkar.”

Da yake gabatar da tasa makalar, Shugaban Jami’ar Jihar Kogi Farfesa Muhammad Sani Abdulkadir, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kara yawan kudaden da take ware wa hukumomin tsaron kasar domin ci gaba da yaki da ta’addanci da sauran miyagun laifuffuka da ake aikatawa a fadin kasar nan, wanda ya ce zai karfafa musu gwiwa wajen sauke nauyin da tsarin mulki ya daura mata.