Magoya bayan Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, sun yi da zanga-zanga a Hedtikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na jihar.
Shugaban kungiyar, Abdurrahman Bobbo ya yi wannan alwashi ne a gangamin goyon bayan Fintiri da wasu kungiyoyi 75 suka shirya a Yola a ranar Laraba.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabon Tsarin CBN Zai Raba Mutane Da Ayyukansu
- Bene mai hawa 7 da ake aikin gina shi ya rushe a Legas
Ya ce ’yan jihar za su yi da gaske wajen kare kuri’usu gare shi, duk kuwa da irin adawa da yake fuskanta.
“’Yan Adamawa ba za su taba bari a sace kuri’ar da suka jefa wa da Fintiri ba; za su mamaye hedikwatar INEC daga ranar Asabar har zuwa lokacin da za a ba Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri takardar shaidar lashe zaben,” inji shi.
Yayin da yake nanata kudurinsu na tabbatar da an yi abin da ya dace, Bobboi ya ce kishin jama’a zai yi galaba a kan muradun wadanda suka samu umarni daga sama na lalata tsarin zabe da ’yancin jama’a.
Ya ce da wuya PDP ta fadi zaben gwamnan ba duba da cewa kuri’u 31,000 da ke tsakaninta da APC musamman ma ganin cewa rumfunan zabe da za a yi zabe na da kuri’u 42,000 kacal.
Bobboi ya kara da cewa jihar Adamawa ta PDP ce shi ya sa ta doke APC a zabukan da aka yi kuma a bayyane yake cewa za ta lashe wanda ke tafe.
“PDP na da biyu daga cikin zababbun sanatoci uku, tana da bakwai daga cikin zababbun ’yan Majalisar Tarayya da kuma 15 cikin 25 na zababbun ’yan majalisar dokokin jiha; Don haka ba za a yi tunanin ta fadi zaben gwamna ba.
“Yan Adamawa suna bayan gwamnan; abin da muke nema shi ne tsarin zabe na gaskiya da adalci wanda zai tabbatar da nasararmu a ranar Asabar.
“Za mu gabatar da bukatunmu ga INEC da kuma gwamna,” inji Bobboi.
Da yake mayar da martani ga kungiyoyin, Awwal D. Tukur wanda ya nemi takarar gwamnan ya gode musu bisa yadda suke kare dimokuradiyya.
Idan dai za a iya tunawa INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba saboda yawan kuri’un da aka soke a wasu rumfuna na iya sauya sakamakon.
Sakatariyar INEC, Anthonia Adamu ta shaida wa masu zanga-zangar cewa hukumar za ta gudanar da zaben adalci inda ta sanya hannu a takardar da jam’iyyar ta kawo mata.