Malama Hajara Ahmad Hussaini ta lashe Gasar Gajeren Labarai na Hikayata na BBB Hausa na Shekarar 2024.
Malama wadda ta zama Gwarzuwar Gasar Hikayata ne bayan ta yi wa marubuta 450 fintinkau da labarin da ta rubuta mai taken ‘A Ban ’Yanci’.
A daren ranar Laraba aka karrama ta da kyautar Naira miliyan ɗaya da takardar shaidar girmamawa a wani ƙasaitaccen buki da aka gudanar a Abuja.
‘A Ban ’Yanci’ labarin wata matashiya ce da ta sha gwagwarmaya da niyyar ganin cewa ta kawo canji, inda har aka kai ta gidan yari a sanadiyyar hakan.
Sauran waɗanda suka rufa mata baya a cikin marubuta a Gasar Hikayata da aka tsara domin bunƙasa ɗabi’ar rubuce-rubuce a tsakanin mata su ne Amra Awwal Mashi, wadda ta zo ta biyu da labarinta mai suba ‘Ƙura A Rumbu’, inda ta samu kyautar Naira dubu 750 da takardar shaidar girmamawa.
Wadda ta zo ta uku ita ce Zainab Muhammad Chubdo, da labarinta mai suna ‘Tsalle Ɗaya’, inda aka ba wa kyautar Naira dubu 500 da takardar shaidar girmamawa.