✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben 2023: Obi ya lallasa Atiku a Delta

Obi ya yi wa abokin takarar Atiku zarra a Jihar Delta da yake zaman gwamna.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kayar da takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben da ya gudana ranar Asabar a Jihar Delta.

Hakan dai na kunshe ne cikin bayanan da Baturen Zaben Jihar, Farfesa Owunari Abraham Georgewill ya gabatar a Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe ta Hukumar INEC da ke Asaba.

A cewar Farfesa Owunari, Obi ya samu kuri’u 341,866 yayin da bai wa Atiku tazara da kuri’u 180,266 wanda ya samu kuri’u 161,600 kacal.

Wannan lamari ya zo a ba-zata kasancewar abokin takarar Atiku, Ifeanyi Okowa, shi ne gwamna mai ci a jihar.

Ga yadda sakamakon zaben ya kaya:

ADC -160
ADP -788
APC -90,183
APGA -3,746
APM -1,028
APP -493
BP -1,016
LP -341,866
NNPP -3,122
MRM -988
PDP -161,600
PRP -334
SDP -3,071
YPP -605
ZLP -3,324

Yawan masu zabe da suka yi rajista: 3,225,046

Masu zaɓen da aka tantance: 667,149

Adadin sahihan kuri’u: 615,341

Kuri’un da aka soke: 39,309

Kuri’un da aka kada: 654,650