Jam’iyyu 14 ne ke hankoron kujerar gwamnan Kano yayin da tuni kowacce daga cikinsu ta tsayar da dan takara da zai fafata a zaben 2023.
An lika jerin sunayen jam’iyyun da ‘yan takararsu a babban ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Jihar Kano.
- An kashe mutane 645 cikin watanni shida a Kaduna
- Ba na garkuwa da mutane sai dai kawai na kashe su —Aleiro
Takardun da INEC ta manna a allunan bayananta, ya kuma kunshi jerin sunayen ‘yan takarar mataimakin gwamna, wanda ya yi daidai da yadda Dokar Zabe ta tanadar.
Haka kuma, jerin ya kunshi sunayen ‘yan takarar Majalisar Dokokin Jihar da a kan manna a ofisoshin INEC da ke mazabu 40 a fadin jihar.
Jam’iyyun da za su yi takara su hada da; APC, PDP, New Nigerian Peoples Party (NNPP), Peoples Redemption Party (PRP), Allied Peoples Party (APP), da Zenith Labour Party (ZLP).
Sauran sun hada da; Social Democratic Party (SDP), Action Peoples Party (APP), Labour Party (LP), National Rescue Party (NRP) da African Democratic Congress (ADP).
Ragowar kuma su ne APGA, Action Alliance (AA) da African Action Congress (AAC).
Aishatu Mahmud ta jam’iyyar NRP ita ce mace tilo da ta tsaya takarar kujerar gwamnan, yayin da Fatima Muhammad ta kasance mace tilo da ke takarar mataimakiyar gwamna a karkashin jam’iyyar Action Alliance (AA).
Shahararren malamin addinin musuluncin nan na Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, yana cikin masu takarar a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Haka kuma, Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf-Gawuna, shi ne dan takarar jam’iyyar APC, yayin da Alhaji Abba Kabir-Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba Gida-gida”, ke takara a jam’iyyar NNPP.
Aminiya ta ruwaito cewa, Sadiq Wali shi ne sunan da ya bayyana a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP, a maimakon Mohammed Abacha wanda a baya INEC ta tabbatar da cewa shi ne dan takarar jam’iyyar.
Sai dai da yake martani kan wannan takaddama, mai magana da yawun INEC na Jihar Kano, Adam Ahmad Maulud, ya ce sanya ido kan lamuran da shafi gudanar da zaben fitar da yan takara shi ne nauyin da rataya a wuyansu.
Maulud ya ce wannan sunayen da aka gani hukumar ta manna a bango ranar Juma’a shi ne abin da aka dawo musu da shi daga hedikwatar hukumar da ke Abuja.
“Mun aika da abin da muka yi zuwa hedkwatarmu ta kasa kuma abin da muka lika a yau [Juma’a] ya fito ne daga gare su kai tsaye.”