Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce babu wani tanadin tsarin karba-karba na Shugabancin Kasa da jam’iyyar APC ta yi dangane da zaben 2023 illa iyaka ya kamata ta yi amfani da duk wani tsari da ke kan gaskiya da adalci.
Shekarau wanda ke wakilcin shiyyar Kano ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin amsa tambayoyin manema labarai dangane da tsarin da jam’iyyarsu ta APC za ta yi amfani da shi wajen zaben Shugaban Kasa a 2023.
- Bayan shekaru 15 Bafarawa ya kai ziyara gidan Wamakko
- Satar Mutane: Sheikh Gumi ya ziyarci garuruwan da suka yi kaurin suna a Kaduna
- Yadda aka yi na zama Minista a Gwamnatin Jonathan — Bala Mohammed
Ya ce ya yarda da duk wani tsari mai dauke da ka’ida ta gaskiya da adalci yana mai cewa, “akwai kundin tsarin mulki na hankali da tunani, wanda dole ne mutane su yi amfani da shi.
Sardaunan Kano ya ce tsarin karba-karba na kujerar shugabancin Najeriya a tsakanin shiyoyi shida da kasar ta kunsa, ba bu tanadinsa a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan saboda haka bai kamata ya zama hujja ba wajen tsayar da dan takara a jam’iyya.
“Ba na magana ko da’awar tsarin karba-karba, kuma babu wata jiha ta ba ta da daruruwan ’yan takara abin da na yarda da shi a Najeriya a yanzu shi ne zabar Shugaban Kasa wanda ya cancanta ba tare da la’akari da Jiha ko yankin da ya fito ba.”
Shekarau ya kuma yi tsokaci kan alakarsa da wanda ya ci gajiya kuma magajinsa a kujerar gwamnatin Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya ce, “Da ni da Kwankwaso aminan juna ne, sai dai watakila akidarmu ta siyasa za ta iya bambanta amma dukkaninmu daga Jihar Kano muka fito,” inji shi.