✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben 2023: Atiku ya ciri tuta a Sakkwato da Taraba

Peter Obi ne ya zo na biyu a Jihar Taraba da kuri’u 147,315.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana dan takarar Shugaban Kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe Jihar Sakkwato.

Babban jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Kabiru Bala, wanda shi ne Shugaban Jami’ar ABU Zaria ne ya gabatar da sakamakon a ranar Talata.

Atiku ya samu kuri’a 288,679 yayin da Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 285,444.

Sauran ’yan takarar da ke sahun gaba da sun samu:

Dan takarar LP, Peter Obi, ya samu kuri’u 6,568, yayin da takwaransa na NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu kuri’u 1,300.

Kazalika, INEC ta ayyana Atiku a matsayin wanda ya ciri tuta da mafi yawan kuri’u a Jihar Taraba.

Da yake sanar da sakamakon zaben, Shugaban Jami’ar Tafawa Balewa, Farfesa Muhammad Ahmed Abdul’aziz, ya ce dan takarar na PDP ya samu kuri’u 189,017.

Dan takarar jam’iyyar Labour ne ya zo na biyu a jihar da ke Arewa maso Gabas da kuri’u 147,315.

Jam’iyyar APC ce ta zo a mataki na uku da kuri’u 135,165, yayin da NNPP ta samu kuri’u 12,818 kacal.

Farfesa Abdul’aziz ya bayyana zaben a matsayin wanda aka gudanar cikin lumana kuma na gaskiya da adalci.