Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, Uban jam`iyya mai mulkin Najeriya ta APC, tsohon Gwamnan Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ne zai jagorancin ragamar kamfen din takarar shugabancin Najeriya da yake nema a karo na biyu.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin kaddamar da kamfen dinsa da aka yi a Abuja.