Huduba ta Biyu:
Bayan yabo da godiya ga Allah.
Ya ku bayin Allah! Lallai na daga cikin abin da hudubarmu ta yau take tsokaci a kai cewa; “Ba za ka taba samun mutanen kirki masu gaskiya suna zabe ko goyon bayan zulunci da azzaluman shugabanni ba.”
Ya ku bayin Allah masu girma! Mu sani, Allah (SWT) Ya yi umarni da adalci da goyon bayan adilai a duk inda suke, sannanYa yi hani da zalunci da goya wa zalunci da azzalumai baya a duk inda suke. Allah (SWT) Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma cewa: “Lallai Allah Yana yin umurni da adalci da kyautatawa da umurni a bai wa ma’abucin zumunta, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi muku gargadi, tsammaninku kuna tunawa.” (Nahli: 90)
Sannan Allah Yana cewa: “Kada ku karkata zuwa ga (ku goyi baya/ko ku zabi) wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku (tare da su). Kuma ba ku da wadansu majibinta baicin Allah, sannan kuma ba za a taimake ku ba.” (Hud:113).
Ya ku Musulmi! Lallai cikin wadannan ayoyi masu girma, mun ga yadda Allah Ya umurce mu da tsaida adalci da kuma cewa kada mu yarda mu goyi bayan azzalumai. Mahaliccinmu Ya tabbatar mana da cewa in har muka ki bin umurninSa, to, lallai azabar wuta za ta shafe mu tare da azzaluman da muka goyi bayansu.
Ya ku bayin Allah! Mu kalli rayuwarmu a yau, shin muna bin umurnin Allah kuwa? kiri-kiri za ka ga mutum ya goyi bayan azzalumi ba don komai ba, wai sai don jam’iyyarsu daya ko yarensu daya, ko addininsu daya, ko garinsu daya, ko jiharsu daya, ko kasarsu daya, ko yanki daya suka fito. Shin wannan mummunar dabi’a za ka same ta a wurin mutumin kirki kuwa? Yau an wayi gari ba mu kyamar zalunci da azzalumai saboda kwadayin abin duniya da son zuciya.
’Yan uwa Musulmi masu girma! Mu kalli yadda zaluncin cin hanci da rashawa suka yi katutu a Najeriya, Allah Ya albarkaci wannan kasa da duk nau’in albarkatu, amma saboda zalunci da cin hanci da rashawa da rashin adalcin shugabanni, an wayi gari kasar tana neman rushewa. A yau kowane fanni ka duba za ka ga ba inda zalunci bai yi katutu ba. To bayan wannan, babban bala’in ma shi ne goyon bayan masu zaluncin don abin duniya, ko don wata bukata ta mutum shi kadai. Sai wannan ya jawo ba a gudun aikata zalunci domin mutane sun san duk zaluncin da za su yi, duk satar da za su yi, matukar suna da abin hannu, to al’umma za ta karbe su hannu bibiyu, a girmama su, a ba su sarautun gargajiya ko digirin girmamawa ko wani matsayi a cikin al’umma.
Saboda haka ya ku ’yan uwa! Ku sani, lallai idan aka wayi gari al’umma ta zama haka, to sai dai a ce Allah Ya kiyaye, domin tabbas Allah zai jarrabi wannan al’umma da abubuwa marasa dadi masu yawa, kamar yadda muke gani a yau. Allah Ya kare mu, amin.
Ya ku ’yan Najeriya! Lokaci ya yi da za mu dakatar da wannan mummunar dabi’a a tsakaninmu domin Allah Ya dube mu da idon rahama, kuma Ya tausaya mana, Ya kawo muna karshen wadannan bala’ o’i da suka addabe mu musamman rashin tsaro da sauransu.
Ya ku musulmi! Mu duba saboda munin zalunci, Allah Ya ce lallai Ya haramta wa kanSa zalunci, kuma Ya sanya shi ya zama haramun tsakaninmu, saboda haka ya ce, kada mu zalunci juna. Amma duk mun manta da umurnin Allah, an wayi gari muna goyon bayan azzalumi saboda dan uwana ne, ko addininmu daya, ko dan jami’yyata ne, ko yarena ne, ko don kwadayin abin hannunsa. Kuma da wannan mummunar dabi’a, wai mu ce mu Musulmin kwarai ne, ko mu ce mu mutanen kirki ne! Shin muna nufin za mu yaudari Allah ne? Ya kamata mu shiga taitayinmu domin Allah ba abin wasa ba ne.
Ya ku bayin Allah! Imam Ibnu Kasir a yayin da yake bayani game da ayar nan da ta yi hani a kan goyon bayan azzalumai da ke cikin Suratul Hud: 113, ya ce: “Fadin Allah cewa,” Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku.” Aliyu bin dalha ya ruwaito daga dan Abbas cewa, ma’anarta: “Kada ku mika wuya ga azzalumai.”
Kuma Imam Al-Aufiy ya ruwaito daga dan Abbas, cewa: ma’anarta ita ce, “Kada ku karkata da goyon bayan shirka da zalunci.” Kuma Abul-Aliyah ya ce, ma’anarta, “Kada ku yarda da aikin zalunci da ayyukan azzalumai.” Shi kuwa Imam Ibnu Jarir ya ruwaito daga dan Abbas cewa, ma’anarta: “Kada ku karkata ku goyi bayan azzalumai.” Daga karshe Ibnu Kasir ya ce, zance mafi kyau game da fassarar wannan aya, shi ne; “Kada ku taimaki azzalumai a kan zaluncinsu, ta hanyar goyon bayansu. Domin duk wanda ya aikata haka, to ya yarda da aikinsu na zalunci ke nan.”
Ya ku Musulmi masu sauraro! Lallai mu san wannan aya ta kai matuka wajen hani a kan zalunci da goyon bayan azzaluman shugabanni. To idan har Allah Ya yi tanandin azabar wuta ga wanda ya karkata ga azzalumai ko yaya ne, to ina ga wanda ya yi dumu-dumu cikin goyon bayansu ta hanyar yi musu kamfen na siyasa da sauransu don abin da zai samu a hannunsu?
Ya ku Musulmi masu girma! Lallai mu sani, ko shakka babu goyon bayan zalunci da azzalumai haramun ne, Allah Ya hana. Sannan yana daga zunubai masu girma, (Kaba’irai). Domin Allah Ya yi alkawarin narkon azaba a kan wannan. Sannan mu sani, abin da kawai ya halatta mu yi ga azzalumi, shi ne mu taimake shi mu hana shi yin zaluncin, idan shugaba ne mu hana shi ci gaba da shugabancin ta hanyar da doka ta yi tanada, wato zabe.
Imam Al-Zamakhshari ya ce: “Hani a kan goyon bayan azzalumai ya hada da kada ka shiga cikin bin son zuciyarsu, ka nisance su, kada ka yi abokantaka da su, kada ka zauna da su, kada ka ziyarce su, kada ka yi shiru a kan zaluncinsu, kada ka nuna amincewarka a kan zaluncinsu, kada ka yi kamanceceniya da su, kada ka kwaikwaye su ta kowace fuska, kada ka yi kwadayin abin hannunsu, kada ka yabe su har ka nuna cewa su masu girma ko masu mutunci ne, sannan kada ka nemar musu jama’a da magoya baya (wato yi musu kamfen idan su ’yan siyasa ne).”
Kuma an haikaito cewa: “Babban malami daga cikin magabata da ake kira Al-Muwaffik, wata rana yana Sallah a bayan wani limami, sai limamin ya karanta Suratul Hud, da ya kawo daidai aya ta 113 inda Allah ke maganar “Kada ku karkata ku goyin bayan azzalumai, idan kun yi haka wuta zata shafe ku.” Sai wannan bawan Allah (Al-muwaffik) ya fadi a kasa magashiyan ya suma, a lokacin da ya farfado sai aka tambaye shi, gafarta Malam me ya faru ne? Sai ya ce, “Wannan ayar tana nufin Allah zai azabtar da wanda ya goyi bayan azzalumi ne, to ina ga azzalumin shi kansa?” Sai ya ce wannan shi ne na tuna sai ya tsoratar da ni, hankalina ya tashi ya sa na suma.”
Saboda haka ya ku ’yan Najeriya! Mu ji tsoron Allah, kuma mu sani wallahi ba zamu kawo karshen zalunci ba, har sai mun daina goyon bayan mulkin azzalumai mulkin danniya. Sai mun kyamace su da abin da suka mallaka. Amma muddin azzalumi zai yi zalunci ya tara abin duniya ta hanyar zaluncin, kuma mu je muna kwadayin wannan abin nasa, muna girmama shi saboda abin duniya, to ba yadda za a yi zalunci ya kare a cikin al’umma.
Ya ku ’yan Najeriya! Ku sani, lallai zaben 2015 yana kusantowa, wannan lokaci mai matukar muhimmanci ne ga rayuwarmu, lokaci mai tsada yana karatowa. Wane irin shiri da tanadi muke yi domin zuwan wannan lokaci? Shin mun san muhimmanci da tasirin zaben shugabannin kwarai ga rayuwarmu kuwa? Shin za mu sake yarda da duk wani mayaudari kuwa? Shin za mu ci gaba da jefa rayuwarmu da ta ’ya’yanmu da jikokinmu cikin hadari ne? Shin har yanzu barci muke yi ko mun farka? Shin za mu yarda mu ci gaba da rayuwa cikin kaskanci da wulakanci ne? Shin za mu yarda mu ci gaba da rayuwa irin ta bayi? Duk amsoshin wadannan tambayoyin da sauransu za mu fahimce su ne a zaben 2015, in Allah Ya sa muna raye.
Mu duba yadda tsananin yunwa da fatara da talauci da cututtuka da rashin tsaro da rashin hanyoyi masu kyau da rashin kyakkyawan ruwan sha da rashin magani a asibiti da rashin ingantattun makarantu jahilci, yara ba karatu, marasa lafiya ba kudin magani, addini ba kulawa, marayu da gajiyayyu an yasar da su, duk da irin dimbin arziki da masu arzikin da Allah Ya hore wa kasar nan. Wai a cikin irin wannan hali da yanayi ake son mu yi fatar tabbatuwar wannan irin bakin mulki, mulkin da babu kwarewa ba tausayi da imani a cikinsa!
Ya ku Jama’a! Lallai ya zama wajibi a kan duk wani dan Najeriya ya yi wani abu domin samun canjin shugabanci a wannan kasa. Ya zama dole mu zabi shugaba adili, mai kishin kasa, mai son ’yan kasa, mai kokarin hada kan ’yan kasa, jarumi, gwarzo, mara tsoro, wanda ya fahimci kasar nan, wanda zai bai wa kowa hakkinsa ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Idan kuwa mun ki ji, mun bi soye-soyen zukatanmu, to ba za mu ki gani ba.
Allah ba ruwanSa, Ya riga Ya ba mu dama, Ya kuma ba mu zabi, idan har muka yi amfani da damar ta hanyar da ta dace, mu ne za mu amfana, idan muka banzatar da damar, za mu ci gaba da shan wahala. Allah ba zai sauko Ya zabar mana shugabanni na kwarai ba, mu ne za mu yi don haka ya rage namu.
Imam Murtada Muhammad Gusau,
08038289761, imel [email protected] ko [email protected]