✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zabe: Gwamnati ta ba da umarnin rufe iyakokin Najeriya

An takaita zirga-zirga zuwa rumfunan zabe kadai

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe ilahirin iyakokin kasa ’yan sa’o’i kafin zaben da za a gudanar ranar Asabar.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ce an dauki wannan mataki ne domin hana ’yan kasashen waje yi wa harkokin zaben Najeriya katsa-landan.

Sanarwar da mai bai wa ministan shawara, Sola Fasure, ya fitar a ranar Juma’a ta ce, “An takaita zirga-zirga zuwa rumfunan zabe kawai.

“Haka ma an hana zirga-zirga a iyakokin kasa.

“An bukaci jami’an tsaro su bai wa rayuka da dukiyar ’yan kasa kariya a mazabu da hanyoyi da kuma kan iyakokin kasa.”

Aregbesola ya yi kira ga ’yan kasa da su fito su kada kuri’a a ranar Asabar.

Ya kuma ba da tabbacin za a bai wa mutane kariya da kyakkyawar kula lokacin zabe da ma bayan zabe.

Kazalika, ya bukaci jama’a da su kasance masu lura da kuma kai rahoton duk abin da ba su yarda da shi ba a lokacin zaben.