Hadimin Shugaban Kasa kan yada labarai, Garba Shehu ya ce manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Zabarmari, Jihar Borno ba su da izinin zuwa gona daga sojoji lokacin da aka afka musu.
Garba Shehu ya bayyana haka yayin tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC ranar Litinin, inda ya ce, “ba na zargin manoman da aka kashe amma kuma fa dole a fadi gaskiya”.
- Zabarmari: A gabana aka yi ta yanka ’ya’yana —Mahaifi
- Manoma 110 ne aka kashe a Zabarmari —MDD
- Kisan Borno: Sojoji sun musanta rahoton MDD
Ya ce: “Gwamnati ta yi bakin ciki da kisan manoma 43 da ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda galibinsu ’yan ta’addan suka yi wa yankan rago.
“Ya kamata mutane su san abun da ya faru a yankin Tabkin Chadi: Galibin irin wadannan yankunan wurare ne da ’yan Boko Haram suka mamaye da har yanzu akwai wuraren da ba a kammala kakkabe ragowar ’yan ta’addar ba ballantana mutanen da ke yankin kauyukan su samu damar komawa.
“Akalla irin wadannan wuraren akwai bukatar a samu izinin komawa wuraren daga rundunar soji kafin manoma su samu kwarin guiwar komawa su ci gaba da harkokinsu”, inji Garba Shehu.
Da yake bayar da amsa kan cewa baya zargin manoman da aka halaka a yankunan, Garba Shehu ya ce, ya kamata manoman su samu izini daga sojoji da ke kula da yankin.
“Ba lallai hakan ta faru ba amma gaskiya dai dole a fade ta. Shin sun nemi izini daga sojojin da ke kula da yankunan, sun tambayi wani cewa suna son komawa harkokinsu?
“Na fada wa su shugabannin sojojin cewa ba sa jin shawara, tabbas su ’yan ta’addar za su iya amfani da wannan gabar su afka musu”, inji shi.
Ya ce, akwai wurare a Jihar Borno da ’yan ta’adda suka barnata da ya kamata mutane su guje su har sai sun samu tabbaci da izinin komawa daga sojoji.
“Jami’an soji ba lallai a ce kan idonsu komai zai faru a ko’ina ba. Ko da kuwa mutane suna son komawa wuraren su don ci gaba da harkokinsu na noma ya kamata su samu izini kafin komawa bakin aiki”, inji shi.