✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu hukunta lauyan Abdujabbar kan cin mutuncin alkali —Kotu

Ana zargin Barista Dalhatu da cin mutunci da kuma raina kotu a shari'ar Abduljabbar,

Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano karkashin jagorancin Mai sharia Tijjani Yakasai ta sha alwashin ladabtar da lauyan Abduljabbar Kabara, Barista Dalhatu Shehu Usman, bisa maganganun bata suna da ya furta a kan alkalin da ke sauraron shari’ar malamin, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola.

Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun Kotunan Shari’ar Musulunci na Jihar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya sanya wa hannu.

A cewar takardar, a zaman kotun wacce ke Kofar Kudu a Jihar Kano, lauyan Abduljabbar Kabara din, Barista Dalhatu Shehu Usman ya yi wasu kalamai na cin mutunci ga aikin shari’a wanda kuma hukumarsu ba za ta kyale ba.

“Lauyan ya fadi abubuwan da ke ransa game da alkalin wanda kuma yin hakan raini ne ga kotu, wanda bai kamata a ce masanin shari’a ne zai furta irin wadannan kalamai a harbar kotu ba.

Har yana cewa wai alkalin umarni ake ba shi wai kuma a cewarsa alkalin yaron Karibu ne.”

Muzammil Ado Fagge ya kara da cewa hukumarsu ba za ta nade hannu ta zuba ido ana cin mutunci shari’a da alkalai ba.

Don haka ya zame mata dole ta dauki matakin shari’a akan lauyan.

Sannan, hukumar ta yi kira ga Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, reshen Jihar Kano da ta gaggauta daukar mataki a kan lauyan bisa abin da ya aikata na batanci ga harkar shari’a.