Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta sa ido yadda ya kamata wajen ganin ba a sami hauhawar farashin kayan abinci a sabuwar shekarar 2021 ba.
Ya yi alkawarin ne yayin taron Majalisar Shugaban Kasa Kan Ba da Shawara a Harkokin Tattalin Arziki karo na biyar da ya gudana a Fadar Shugaban Kasa ranar Talata.
- Na kan ji takaici duk lokacin da aka kai wa ’yan Najeriya hari —Buhari
- Duk da bude wasu iyakoki, har yanzu babu damar shigo da shinkafa da kaji
Shugaban ya kuma umarci Babban Bankin Kasa (CBN) da kada ya kuskura ya ba masu shigo da abinci canjin kudaden kasar waje.
“Yanzu haka, akalla jihohi bakwai na iya noma shinkafar da muke bukata. Dole mu ci abinda muke nomawa,” inji Buhari.
Ya kuma yi jawabi kan irin nasarorin da aka samu a harkar noma sakamakon manufar gwamnatinsa na fadada tattalin arzikin kasa ta hanyar rage dogaro a kan man fetur
Buhari ya ce yana mamakin halin da Najeriya za ta iya tsintar kanta a halin matsin tattalin arzikin da annobar COVID-19 ta jefa jama’a idan da kasar ba ta rungumi harkar noma ka’in da na’in ba.
Shugaban ya ce, “Za mu ci gaba da karfafa gwiwar mutane su koma gona. Masu kudin mu da dama sun dauka cewa tunda muna da arzikin mai sun yi watsi da gona sun garzayo birane saboda su ci kudin mai. To yanzu mun koma gona.
“Yanzu ku yi tunanin abinda zai iya faruwa da ba mu habaka harkar noma mun rufe iyakokin mu ba. Da mun shiga garari matuka,” inji shi.
Taron dai ya mayar da hankali ne wajen tattauna kalubalen da tattalin arzikin kasa da ma na duniya baki daya ya shiga a shekara mai karewa ta 2020.
Ya kuma sami halartar Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Ministar Kudi, Zainab Ahmed ta takwararta ta Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar-Farouk.