✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi murna idan Buhari ya cika alkawarin da ya yi mana shekara 30 da suka wuce -dan kwallon Eaglet Yahaya Muhammad

Yahaya Muhammad yana daya daga cikin matasa ’yan kasa da shekara 15 da suka lashe kofin duniya karo na farko a kasar Sin a shekarar…

Yahaya Muhammad yana daya daga cikin matasa ’yan kasa da shekara 15 da suka lashe kofin duniya karo na farko a kasar Sin a shekarar 1985 da aka yi wa lakabi da ‘CHINA 85’.  Bayan da suka mika wa Shugaban kasa na wancan lokacin kofin a fadar gwamnati da ke Dodan Barracks Manjo Janar Muhammadu Buhari ya yi musu alkawurra. Wakilinmu ya samu tattaunawa da daya daga cikin matasan a wancan lokaci wato Yahaya Muhammad domin jin ta bakinsa game da wannan albishir. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ya ya ka ji lokacin da aka sanar cewa Shugaban kasa  Muhammadu Buhari zai cika alkawarin da ya yi muku shekara 30 da suka wuce?
 Yahaya: Da farko dai ina mika godiya ga Allah Madaukakin Sarki wanda ya nuna mana wannan lokacin cikin koshin lafiya.Tunda aka sanar da cewa  Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa na yi addu’o’i masu yawa da fatan alheri a gare shi.  Dalili kuwa shi ne a shekarar 1985 da muka lashe kofin duniya a karo na farko da Hukumar Kula da  kwallon kafa ta Duniya FIFA ta shirya a kasar Sin watau China ke nan, da muka shiga wurinsa a fadar gwamnati, sai na ga ya burge ni don kuwa na ga shuagabana babu shamaki a tsakaninmu, kuma mun yi musabaha da juna tare da taya mu murnar nasarar da muka samu. Mutum ne wanda ya iya bakinsa, kamili wanda da dadewa ya shiga cikin dattawan duniya. Don haka ban yi mamaki ba da na samu labari a kafofin watsa labarai cewa ya lashi takobin cika alkawarin da ya yi mana a baya .Magana ta gaskiya ba mu ba shi laifin rashin cika alkawarin ba, don kuwa ya yi mana alkawarin babu dadewa aka yi masa juyin mulk.
Aminiya: Wadanne alkawurra ya yi muku?
 Yahaya: Kafin in kai ga amsa wannan tambay, bari in tuna wa ’yan Nijeriya cewa  Muhammadu Buhari ne ya rada wa wannan kungiya suna Golden Eaglets.Abinda ya faru shi ne, lokacin da aka hada kungiyar an ba ta suna Baby Eagles ne. Da wannan sunan muka je kasar Sin muka fafata a gasar daga wasan farko zuwa na karshen da muka doke kasar Jamus sannan muka lashe kofin. Da yake yi mana jawabi a lokacin da yake yi mana maraba  ne ya shaida wa duniya cewa daga ranar ya cana mana suna daga Baby Eagles zuwa Golden Eaglets. Ka ji sanadiyyar sunan ke nan. Game da alkawurra kuwa, ya nemi gwamnonin jihohi 19 na lokacin da su karrrama mu kuma su ba mu tukuici. Bayan haka kuma a sanya sunan kowane daya daga cikinmu a titunan jihohinmu.  Sannan a sai mana hannayen jari a wasu kamfanoni tare kuma da ba mu tallafin karo karatu a manyan makarantu. Sai kuma a ba mu filaye a jihohinmu, ko gidaje.  Sannan ya bayar da umurnin a tabbatar mun je kasar Medico  don mu kalli gasar cin kofin duniya na manya wato Medico 86 World Cup.
Aminiya: Wadanne ne daga cikin wadannan alkawurra za ka iya tunawa an cika muku su?
Yahaya:  Na samu tallafin karo ilimi a Makarantar Koyar da Ilimin kere-kere ta Gwamnatin Tarayya da ke Kaduna. Sai kasar Medico da aka kai mu in da muka kalli wasu daga cikin wasannin cin kofin duniya.  Sannan an sanya sunana a wani titi a Minna na Jihar Neja  kodayake  a shekarar 1991 gwamnatin jiha a wancan lokaci ta cire sunana daga kan titin,.  Ka san yadda harkokin siyasa ke tafiya a kasar nan sai a hankali.
Aminiya: Wadanne alkawura ne ba a cika muku ba?
 Yahaya: Ba a sai mana hannun jari ba sannan ba mu yi rangadin jihohi 19 na wadancan lokacin ba. Ba a tanadar mana gidaje ko filayen da ya bayar da umurnin a yi ba, sannan an hana mu rattaba hannu a duk wata kwangila da manyan kungiyoyin kwallon kafa a kasahe daban-daban na duniya wadanda suka nuna sha’awar suna so mu yi musu wasa. Jami’an wancan lokacin suka ce mana ba mu da ’yancin haka don mu mallakar gwamnatin tarayya ne.
Aminiya: Me kake gani ya janyo matasan kungiyar U-17 suka samu nasarar lashe kofin a bana a kasar Chile?
Yahaya: A nawa ra’ayin abubuwan da suka sa suka samu wannan nasarar sun hada da na farko sun dade suna tare, sannan masu horar da su san abinda suke yi. Bayan haka yaran suna gyara kura-kuran da suka tafka yayin da suke wasa. Babban abinda na tuna lokacin da yaran nan suka daga kofin nan, na tuna lokacin da muka yi makamacinsa a kasar China.
Aminiya: An tuntube ka game da maganar da Shugaban kasa ya yi na cika alkawarin da ya yi muku?
Yahaya: kwarai da gaske an turo wata tawagar gwamnatin tarayya ta zo ta gana da ni da Kocin mu Bala Shamaki. Da suka zo sun yi mana bayanin ko su wanene da kuma dalilin zuwansu. Daga bisani suka yi mana tambayoyi tare da neman karin haske game da wasu al’amura.Mu kuma ba mu boye musu komai ba, muka gaya musu dalla-dalla. Da suka gama,sai suka wuce abinsu suka ce za su tuntube mu
Aminiya: Yaushe ne suka ce za su gayyace ku zuwa Abuja?
Yahaya:  Gaskiya ba su gaya mana ainihin ranar da za mu je ba. Na yi imani da zarar lokaci ya yi za a kira mu. Don kuwa alamu sun nuna haka.
Aminiya: Wadanne shawarwari ne za ka iya ba Shugaban kasa dangane da bunkasa harkar wasanni a kasar nan?
Yahaya: Shawarwarin da zan ba shi sun hada da a samar da isassu kuma ingantattun filayen wasanni. Sannan yakamata a rika yi wa ’yan wasa tanadin kula da lafiyarsu da rayuwarsu ta yadda za su zage damtse don su yi wa kasar nan wasanni a gasannin da ake shirya wa a kasashen duniya.  Abu uku shi ne a samar musu ayyukan yi. Muddin ya yi haka, harkokin wasanni za su bunkasa cikin kankanen lokaci a fadin kasar nan.
Aminiya: Wace shawara za ka ba wadannan zakarun duniya kannenku?
Yahaya: Shawarar da zan ba su ita ce alamu sun nuna cewa manyan kungiyoyin kwallon kafa suna zawarcin wasu daga cikinsu don su yi musu wasa.  Babban abin da yakamata su yi shi ne kar su yi hanzarin rattabawa duk wata kungiya hannu a bisa gaggawa.Ya kamata su yi nazarin takardun kwantiragin cikin natsuwa tare da tuntubar wadanda suka kamata.  Allah Ya sa mu dace. Amin