✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu yi amfani da albarkatun kasarmu mu ciyar da yankinmu gaba – Sarkin kudun Tsafe

Sarkin Kudun Tsafe Alhaji Abubakar Muhammad Abubakar wanda aka fi sani da Abu CBN yana cikin iyayen kasa 16 da ke cikin masarautar Tsafe a…

Sarkin Kudun Tsafe Alhaji Abubakar Muhammad Abubakar wanda aka fi sani da Abu CBN yana cikin iyayen kasa 16 da ke cikin masarautar Tsafe a Jihar Zamfara. A zantawarsa da Aminiya jim kadan bayan nada shi sarautar da sarkin Tsafe, ya yi bayani kan tsarinsa na son ciyar da gudunmursa gaba.

 

Yallabai ko za mu iya sanin tarihinka a takaice? 

Gaskiya na fara karatun Firamare dina a Sakkwato daga na koma Gusau na kammala sai na shiga kwalejin Malamai ta Maru 1973-1978 na yi Sakandare dina, na dan yi karantarwa a firamaren tunfaya kafin na shiga kwalejin horar da malamai ta Jihar Sakkwato C O E. Sanan kuma na tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya in da na yi digiri na farko da na biyu a can a fanin kimiyar na’ura mai kwakwalwa waton Computer science. Na fara aikin gwamnati a matsayin malamin makaranta daga baya na koma ma’aikatar ilmi ta tsohuwar Sakkwato sai aka tura ni makarantar fasaha ta gwamnati da ke Gusau, na zama malami a Jami’ar Ahmadu Bello a fannin lisafi, na yi aiki a bangaren bayanan fasaha na CBN Sakkwato a matsayin Jami’i har na kai mataimakin darakta sashen nema da canja tsaro. 

Yallabai gashi an ba ka sarautar sarkin Kudun Tsafe, za mu iya sanin abin da sarautar ke nufi? 

Sarkin Kudun Tsafe yana daya daga cikin hakiman masarautar Tsafe 16 da ke karkashin mai martaba Sarkin Tsafe Alhaji Muhammad Bawa. Ni ke da hakkin kula da Tsafe ta kudu. 

A lokacin nadinka, sarkin Tsafe ya ce natsuwarka da gudunmuwarka a wurin aiki ya sanya aka ba ka wannan ragamar, wace irin hobbasa ce wannan? 

Ci gaban da na samar wa jama’ata a fanin noma da matasa da ilmi da sauran abubuwa da suke a boye. A kowane lokaci ina karba da bayar da shawara ga sarki tun kafin ya zama sarki, kuma yanzu za mu yi aiki kafada da kafada da shi don mu ga jama’ar mu sun zama masu dogaro da kai. 

Wane shiri kake da shi ga mutanenka don inganta rayuwarsu? 

Abin da zan fi mayar da hankali shi ne yadda za mu iya dogaro da kanmu da albarkatun kasa da Allah Ya hore mana. Kan wannan zan sanya duk wani mai ruwa da tsaki a harkar nan da yake yankinmu mu samar da wani rubutaccen tsari da zamu bi kan yadda za mu yi amfani da albarkatun mu har a samu cigaba. Da yardar Allah nan da shekara biyu zuwa uku za mu fito da shi.  

Kana da kwarewa a fasahar na’ura mai kwakwalwa, ko kana da wani shiri na habbaka wannan baiwar taka ga matasanka?  

Kamar yadda na fadi da farko a shirye nake ga cigaban mutane na. Da yardar Allah zan yi wani abu kan wannan.  

Ko kana da wani kira da za ka yi da ya shafi bukatar gudumwarka da masarautar Tsafe don samun ci gabansu?   

Gaskiya a yanzu duk masu ruwa da tsaki da ’yan kusuwar mu mun tuntube su kuma sun nuna gamsuwa tare da amincewa, za su taimaka a duk lokacin da aka tuntube su ga wani abu da ya taso na cigaban yankin da mutane gaba daya. Kira ita ce mu yi hakuri da lamurran don mu hada hannu mu cimma biyan bukata. Ina kara amfani da wannan damar in nemi mutanenmu da su cigaba da bayar da hadin kai da goyon baya domin mu hadu mu ciyar da yankinmu gaba. Allah Ya taimaka mana.